Allah ya tsare juyin mulkin da ba na kuri’un jama’a ba ne
A cikin makon da ya gabata kafofin yada labaran kasar nan sun ciki sun batse da labaran zargin wasu sojoji na yunkurin juyin mulki a kasar nan da kuma irin martanin da sojojin su ka kai ta bayarwa kafin da bayan taron gaggawar da Babban Hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya yi […]
A cikin makon da ya gabata kafofin yada labaran kasar nan sun ciki sun batse da labaran zargin wasu sojoji na yunkurin juyin mulki a kasar nan da kuma irin martanin da sojojin su ka kai ta bayarwa kafin da bayan taron gaggawar da Babban Hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya yi da Kwamandojin Rundunonin sojojin kasa da manya-manyan Hafsoshinsa a Abuja. Wannan batu na zargin sojoji suna shirin juyin mulki da ya fito daga bakin Hadaddiyar kungiyar ceto yankin Neja Delta ta JNDLF, batu ne da za ka iya cewa a yi wurgi da shi a kwandon shara, a zaman jita-jita ne da masu iya magana kan ce zancen banza, amma bisa ga yadda tsarin kasar nan yake na rashin manufa, mutum ba zai wurgi da shi ba, sai dai idan mai iko ne kuma ya shafe sa ya ce zai bincika, kamar yadda sojojin suke cewa za su bincika don tantance gaskiyar lamari. Marasa iko irin mu, mu tsoma bakunanmu ta irin wannan kafa, sannan kuma mu shiga addu’o’in Allah Ya kare, mu da sauran `yan kasa masu kishinta.
Su dai ’yan kungiyar ta JNDLF, sun yi zargin cewa wasu hafsoshin sojoji suna ta zawarcin neman goyon bayansuwajen aniyarsu (sojojin) ta hambararsa da gwamnati, inda suke zuga su da su ci gaba da saka bama-bamai da wuta a kan bututun man fetur, ta yadda idan sun yi nasara akan juyin mulkin za su dora ’yan kungiyar ta JNDLF a kan mukamai masu maiko. Duk da yake ’yan kungiyar ta JNDLF, ba su fadi sunayen hafshoshin da suka ce suna yawan damunsu da kiraye-kiraye akan su basu goyon baya, domin lambobin wayayoyin da su ke kiran na su sukan boye su, amma dai sun ce harsunansu sun fi kusanci da na Hausawa da Yarbawa.
Hadaddiyar kungiyar ceto yankin Neja Delta din ta yi zargin cewa hanzarin da wadancan Hafsoshi ko masu son a yi juyin mulkin sukan ba ta, wai shi ne, shirin yaki da cin hanci da rashawa da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dukufa a kai ko kusa ba sa jin dadin irin yadda gwamnatin take haska fitilarta kan sojojin, wadanda suka yi ritaya da wadanda suke kan karagar mulki, binciken da sojojin suka ce yana zubar da martaba da kimarsu a idanun `yan kasa. kungiyar ta JNDLF, ta ce “Tuni muka fada wa irin wadancan hafsoshi “mun ki” kuma ba za mu goyi bayansu ba, domin matsalar yankin Neja Delta matsala ce ta siyasa, kuma ta hanyar siyasa kadai za a iya warware ta.” A nan sai suka shawarci Shugaba Buhari da kakkausar murya da ya dauki matakai na gaskiya wajen warware matsalolin yankin, kasancewar ga shi yanzu wasu sojoji suna son su yi amfani da rikicin wajen tada wani rikicin don biyan bukatar kansu.
Bayyanar wadancan zarge-zarge a kan sojojin kasa, ya sanya ba tare da bata lokaci ba mai rikon mukamin Daraktan yada labarai na sojoji Kanar Sani Usman, ya bayar da wata sanarwa a Abuja a ranar Alhamis din makon da ya gabata, inda ya tabbatar da cewa sojoji sun fara bincike don gano tushen wancan zargi mai nauyi na yunkurin juyin mulki da kungiyar ta JNDLF, ta yi, wanda ya ce ba wani abu ba ne illa kamfen din bata suna da tozartarwa da neman mayar da hannun agogo baya daga wadanda ba a san ko su wane ne ba, da ya kira gungun masu aikata manyan laifuffuka da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da suke yi wa sojojin kasar nan, su ke kuma fakewa da kungiyar ta JNDLF.
Kanar Usman ya sake jaddada goyon bayan askarawan kasar ga dukkan turakun mulkin dimokradiyya, wato bangaren Zartarwa da ba Majalisun Dokoki da na shari`a tun daga sama har kasa da kuma shugaban kasa babban Kwamandan askarawan kasar nan. Yana mai cewa ko kusa wannan zargi ba zai kawar da hankulansu ba a kan ayyukansu na yaki da `yan tada kayar baya da sauran ayyukan tabbatar da matakan tsaro a ciki da wajen kasar nan. Yana mai jaddada cewa za su bincika wannan zargi da nufin su gano tushensa da kuma gaskiyarsa.
Bayan kusan sa’o’i 48, da wancan martani na daraktan hulda da jama `a na sojojin, sai kuma ga jawabin Manjo Janar Adeniyi Oyebade, Kwamandan Runduna ta daya,wanda ya biyo bayan wani taron gaggawa da Babban Hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya yi da Kwamandojin Rundunonin kasar nan da wasu manya-manyan Hafsoshinsa, duk dai a kan wancan zargi na wasu hafshoshin sojoji suna yunkurin juyin mulki. Bayan taron, Janar Oyebade ya fada wa manema labarai cewa, taron ya yanke hukuncin lallai su bi diddikin inda wancan zargin ya fito, domin batun ba na a yi watsi da shi ba ne. Ya tabbatar da cewa za su yi amfani da dukkan albarkatun da suke da su don gano tare da tantance inda wancan mugun labari da ake ta yamadidinsa ya fito. Sannan sai ya jaddada goyon bayansu ga dukkan bangarorin dimokuradiyya da Kundin tsarin mulki kamar yadda Kanar Usman ya jaddatar
Waccan zargin wasu hafshoshi za su yi juyin mulki da ya fito daga kungiyar JNDLF da daya daga cikin hanzarin da ta ce sojojin suna kokawa akai wato bincikensu da ake yi akan cin hanci da rashawa, zai iya zama hamzarin ga irin wadancan sojoji, bisa ga irin yadda yanzu gwamnatin ta dage wajen bincikar manya-manyan Hafsoshin sojojin da suka yi aiki a karkashin Gwamnatin Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar`aduwa da ta Dokta Goodluck Jonatahan, irin su Eya Mashal Aled Badeh da dai sauransu a kan irin biliyoyin Nairorin da suka yi rufdaciki a kansu a zamanin mulkinsu.
Hakazalika ko a kwanannan an sallami wasu hafsoshin soja 38, baya ga bincike da ake kai a kan wasu da suka yi ritaya da wadanda suke kan karagar mulki kamar yadda tsarin wannan gwamnati na yaki da cin hanci da rashawa na ba-sani ba-sabo yake.
Idan har ma wasu tsirarun hafsoshi suna jin gangan da gangancin su yi juyin mulki, to, ya kamata irin wadanna hafsoshi su kwana da sanin cewa juyin mulki irin na soja yanzu ya zama tsohon ya yi a duniya. Duk duniya dimokuradiyya ake yayi, kuma duk kasar da ta ce ba ta yin mulkin dimokuradiyya, to, saniyar ware kasashen duniya da kungiyoyinsu za su mayar da ita ta fannoni irin na tattalin arziki da na zamantakewa da sauransu.
Masana kimiyar siyasa da na tattalin arziki sun sha fadi cewa zaman da kasar nan ta yi a karkashin mulkin soja na shekaru aru-aru, su su ka kara jaza ma ta irin mawuyacin halin tabarbarewar tattalin arziki da na zamantake da mana matakan tsaro.
Tun da dai yaki da cin hanci da rashawa na wannan gwamnati ruwan dare ne, kuma duk dan kasa nagari yana maraba da shi. Don haka bai kamata wasu gafalanlun kuma `yan tsirarun hafsoshin soja su ce za su mayar da hannun agogo baya ba. Kafin sojojin su kammala na su binciken shugaban kasa shi ma ya kamata ya kafa na sa kwamitin binciken. Juyin mulkin soja Allah Ya tsaremu, na gindin akwati kuma Allah Ya inganta mana.