Allah Ya yi wa Ahmed Aja Gwarzo rasuwa

Allah Ya yi wa shahararren ma’aikacin Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna (FRCN), Alhaji Ahmed Aja Gwarzo rasuwa.Marigayin dai ya rasu ne a ranar Litinin da ta gabata, bayan ya yi fama da jinya. Ya rasu ne yana da shekaru 69 da haihuwa a gidansa da ke layin Zaurawa a Rigasa, Kaduna.An haifi marigayin ne a […]

Allah Ya yi wa Ahmed Aja Gwarzo rasuwa
Allah Ya yi wa Ahmed Aja Gwarzo rasuwa

Allah Ya yi wa shahararren ma’aikacin Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna (FRCN), Alhaji Ahmed Aja Gwarzo rasuwa.
Marigayin dai ya rasu ne a ranar Litinin da ta gabata, bayan ya yi fama da jinya. Ya rasu ne yana da shekaru 69 da haihuwa a gidansa da ke layin Zaurawa a Rigasa, Kaduna.
An haifi marigayin ne a garin Gwarzo da ke Jihar Kano a shakarar 1946 kuma ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya shida maza biyu mata hudu.
Marigayin ya yi fice ne a shirinsa na Wasa kwakwalwa da yake gabatarwa a gidan rediyon na Tarayya kuma ya yi ritaya daga aiki kafin daga bisani a sake daukarsa a matsayin kwantaragi a gidan radiyon saboda kwarewarsa.
Kadan daga cikin shirye-shiryen da ya gabatar a gidan rediyon a lokacin rayuwarsa sun hada da Cigiya Da Sanarwa da Hajjin Bana da Jakar Magori da Halittun Gida Da Na Daji da Maigida Barka Da Rana da sauransu.
Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.  Da fatan Allah Ya jikansa da rahama.