Allah ya yi wa Alhaji Salihu Ahmadu Birgediya Rasuwa
Allah ya yi wa dan kasuwan nan mai suna Alhaji Salihu Ahmadu, wanda aka fi sani da Birgediya rasuwa a Benin Jihar Edo, bayan fama da jinya na tsawon lokaci da ya yi, kuma shi dan asalin garin jiga Jihar Kebbi. Marigayin ya rasu ya bar matan aure guda uku tare da ‘ya’ya da jikoki.Ance […]
Allah ya yi wa dan kasuwan nan mai suna Alhaji Salihu Ahmadu, wanda aka fi sani da Birgediya rasuwa a Benin Jihar Edo, bayan fama da jinya na tsawon lokaci da ya yi, kuma shi dan asalin garin jiga Jihar Kebbi. Marigayin ya rasu ya bar matan aure guda uku tare da ‘ya’ya da jikoki.
Ance marigayin Alhaji Salihu Ahmadu, wani mutum ne mai son zaman lafiya, tare da jama’a da kuma raha, kamar yadda’yan uwansa da kuma abokan huldarsa, wadanda suka san shi da suka yi harkar kasuwanci tare, suka bayyana shi, da cewa mutum ne mai kyakkyawar dabi’a da sanin ya kamata, kuma yana son sadar da zumunci.
Shi kuwa Sarkin zango, Alhaji Muhammadu Jingudo, wanda ya shaida wa wakilin Aminiya a zaman karbar gaisuwar ta’aziyya ta marigayin cewa: ‘’ Sama da Shekaru 20 da na san marigayi Alhaji Salihu Ahmadu ban taba ganin yana takun saka da wani ba, ballantana a ce an raba shi fada da wani mutum. Don haka zan iya cewa, shi mutum ne mai hankali, kuma mai saukin hali da iya zama da kowa. Lallai mun yi babban rashi. Sai dai in ce Allah ya jikansa da rahama’’.
Kuma tuni an rigaya an yi jana’izarsa a garin Benin, kamar yadda tsarin Addinin musulunci ya tanada. Allah ya gafarta masa, kuma Allah ya ba iyalansa hakuri da dauriya.