Allah Ya yi wa Barde Kerarriyan Zazzau rasuwa

Babban basarake na uku da ya rasu cikin wata daya a Masarautar Zazzau

Allah Ya yi wa Barde Kerarriyan Zazzau rasuwa

Masarautar Zazzau ta sanar da rauswar sabon Barde Kerarriyan Zazzau, Alhaji Buhari Aminu Chiroma.

Sanarwar ta fito ne ranar Talata da dare, inda Masarautar Zazzau ta bayyana kaduwarta da rasuwar tare da fatan Allah Ya yi masa rahama.

“Inalillahi wa inna illaihir rajiun, cikin alhini muke sanar da rasuwar Alhaji Buhari Aminu Chiroma, sabon Barde Kerarriyan Zazzau;  Allahummaghfir lahu warhamhu wa sakkinhu fil jannah,” kamar yadda ta sanar ta shafinta na Twitter.

Babban basarake na uku ke nan da ya rasu a Masarautar Zazzau a cikin kasa da wata guda a cikin shekarar 2021.

Rasuwar Alhaji Buhari Aminu Chiroma na zuwa ne kasa da mako uku da nada shi a sabon sarautar.

Sarki Ahmed Nuhu Bamalli ya ba shi sabuwar sarautar ce a sauye-sauyen da Sarkin ya yi domin cike gurbin manyan saraki biyu da suka rasu a rana guda.

A ranar Juma’a 1 ga watan Janairu, 2021 ne Masarautar Zazzau ta sanar da rasuwar Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu da kuma Talban Zazzau, Alhaji Abdulkadir Pate a lokuta daban-daban.

A watan Satumban 2020 ne kuma Allah Ya yi wa Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris rasuwa bayan ya shekara 45 a kan kargar mulki.

Bayan rasuwarsa ne Sarki mai ci Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya gaji kujerar.