Allah Ya yi wa ‘Bintu’ Dadin Kowa rasuwa
Jarumar ta rasu bayan ta sha fama da rashin lafiya.
![Allah Ya yi wa ‘Bintu’ Dadin Kowa rasuwa Allah Ya yi wa ‘Bintu’ Dadin Kowa rasuwa](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2024/02/images-8-2.jpeg)
Allah Ya yi wa jarumar Kannywood, Fatima Sa’ida wadda aka fi sani da ‘Bintu’ ta shirin Dadin Kowa na tashar Arewa24 rasuwa.
Rahotanni sun bayyana cewar jarumar ta rasu ne a ranar Lahadi, bayan ta sha fama da rashin lafiya.
Wannan na cikin wani sako da Shugaban Hukumar Fina-Finai da Ɗab’i na Jihar Kano, Abba El-Mustapha ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Tuni aka yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, a unguwar Gunduwawa da ke Kano.
Tuni abokan sana’arta suka shiga yi mata addu’a da samun rahamar Ubangiji.
Wasu da dama kuma sun kadu bayan samun rasuwar matashiyar jarumar.