Allah Ya yi wa dan fim Cinnaka rasuwa

A ranar Talatar da ta gabata ce Allah Ya yi wa Baffa Ahmad Cinnaka rasuwa a Wudil jihar Kano.Kamar yadda abokin sana’arsa, Baban Chinedu ya bayyana a turakarsa ta Facebook, ya ce dan wasan ya rasu ne da asuba, bayan ya yi sahur, sai ciwon ciki ya tarnake shi. Ya kara da cewa, an tafi […]

Allah Ya yi wa dan fim Cinnaka rasuwa
Allah Ya yi wa dan fim Cinnaka rasuwa

A ranar Talatar da ta gabata ce Allah Ya yi wa Baffa Ahmad Cinnaka rasuwa a Wudil jihar Kano.
Kamar yadda abokin sana’arsa, Baban Chinedu ya bayyana a turakarsa ta Facebook, ya ce dan wasan ya rasu ne da asuba, bayan ya yi sahur, sai ciwon ciki ya tarnake shi. Ya kara da cewa, an tafi da shi asibiti ne sai ya cika.
Marigayin, wanda aka sani da lakabin Cinnaka a fina-finan Hausa, ya kasance gwani wajen wasannin barkwanci. Ya fito cikin fina-finai, musamman na barkwanci da dama. Yana daya daga cikin wadanda suka rika fitowa fim tare da marigayi Rabilu Musa Ibro da marigayiya Hussaina Tsigai da kuma Lubabatu Madaki.
Tuni dai an yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Muna addu’ar Allah Ya jikansa da gafara, amin.