Allah Ya yi wa dankashi Mai Kukuma rasuwa

Allah Ya yi wa fitaccen makadin kukumar nan Alhaji Muhammadu Sani wanda aka fi sani da Muhammadu dankashi rasuwa. Marigayin mai kimanin shekara 98 ya rasu ne a gidansa da ke Unguwar Ibo Kwatas da ke garin Bauchi, bayan gajeriyar rashin lafiya, a ranar Talatar da ta gabata da yamma.Marigayi Muhammadu dankashi haifaffen kauyen Maina […]

Allah Ya yi wa dankashi Mai Kukuma rasuwa
Allah Ya yi wa dankashi Mai Kukuma rasuwa

Allah Ya yi wa fitaccen makadin kukumar nan Alhaji Muhammadu Sani wanda aka fi sani da Muhammadu dankashi rasuwa.

Marigayin mai kimanin shekara 98 ya rasu ne a gidansa da ke Unguwar Ibo Kwatas da ke garin Bauchi, bayan gajeriyar rashin lafiya, a ranar Talatar da ta gabata da yamma.
Marigayi Muhammadu dankashi haifaffen kauyen Maina Dubabau da ke karamar Hukumar Kabo a Jihar Kano, ya koma garin Bauchi da zama ne fiye da shekara 32 da suka gabata bayan ya yi yawon kade-kade.
Ya rasu ya bar matan aure uku da ’ya’ya biyu tagwaye.
A ranar 3 ga Janairun shekarar 2013 ne Aminiya ta buga hirarsa ta karshe a duniya, inda ya bayyana gwagwarmayar da ya yi a fagen waka, sai dai ya ce ba ya son ’ya’yansa su gaje shi a waka saboda ba ta da daraja a yanzu. Kuma ya shawarci matasa su nemi ilimin addini da na zamani, domin amfaninsu a duniya da Lahira.