Allah ya yi wa Dokta Uba Ahmed Jos rasuwa
Allah Ya yi wa fitaccen dan jaridar nan kuma mai sharhi kan harkokin Gabas ta Tsakiya a manyan gidajen rediyon duniya Dokta Uba Ibrahim Ahmed Jos rasuwa a ranar Juma’ar da ta gabata. Dokta Uba Jos wanda malamin a Jami’ar Jos ne ya rasu ne bayan gajeruwar jinya. An haifi marigayi Dokta Uba Jos ne […]

Allah Ya yi wa fitaccen dan jaridar nan kuma mai sharhi kan harkokin Gabas ta Tsakiya a manyan gidajen rediyon duniya Dokta Uba Ibrahim Ahmed Jos rasuwa a ranar Juma’ar da ta gabata.
Dokta Uba Jos wanda malamin a Jami’ar Jos ne ya rasu ne bayan gajeruwar jinya. An haifi marigayi Dokta Uba Jos ne shekara 52 da suka gabata a Unguwar Nasarawa da ke garin Jos.
Ya yi makarantar Islamiyya Primary school da makarantar Jama’atu Nasril Islam da ke Jos.
Daga nan ya wuce zuwa kasar Sudan ya yi karatun sakandire na shekara uku, sannan ya wuce zuwa kasar Masar a 1988, inda ya shiga Jami’ar Al’azahar ya yi karatun digiri na daya da na biyu da na uku duk a kan Shari’ar Musulunci.
Ya yi aiki da sashin Hausa na gidan rediyon Masar da gidan rediyon Muryar Jama’ar Jamus inda ya zama wakilinsu a yankin Gabas ta Tsakiya.
Marigayin ya yi rubuce-rubuce kan harkokin Gabas ta Tsakiya a jaridun Hausa tare da yin sharhi kan harkokin gabas ta tsakiya a manyan kafofin watsa labaran duniya.
Ya dawo Najeriya a shekara ta 2010 inda ya yi aiki da Jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi, kafin ya dawo da aiki zuwa Jami’ar Jos.
Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya takwas da ’yan uwa hudu. Daga cikin ’yan uwansa akwai Dokta Umar Ibrahim Ahmed.