Allah Ya yi wa Janar Mohammed Wushishi rasuwa
Janar Wushishi ya rasu yana da shekara 81 a Landan, inda yake kula da lafiyarsa
Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Janar Mohammed Inuwa Wushishi ya riga mu gidan gaskiya.
Iyalan marigayin sun ce ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan na kasar Birtaniya yana da shekara 81.
- Mai Shari’a Bolarinwa Babalakin ya rasu yana shekara 94
- Boko Haram ta kai harin ba-zata a rukunin gidaje a Borno
Janar Wushishi ya kasance Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya a Jamhuriya ta biyu, daga 1981 zuwa 1983.
An haife marigayi Janar Wushishi ne a shekarar 1940 a garin Wushishi, hedikwatar Karamar Hukumar Wushishi ta Jihar Neja.
A tsawon rayuwarsa ta aikin soji, ya rike mukamai da dama ciki har da Kwamandan Kwalejin Shugabancin Soji (CSC) da ke Jaji a Jihar Kaduna da kuma Babban Kwamandan Runduna ta 4 na Mayakan Kasa na Sojin Najeriya.