Allah Ya yi wa Malam Bodinga rasuwa

Allah Ya yi wa Malam Abdulmuminu Boɗinga rasuwa a daren Lahadin da ta gabata, inda aka yi masa jana’iza a safiyar Litinin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Marigayin ɗaya ne daga cikin dattawan Kasuwar Mil 12 da ke Legas, inda ya shafe sama da shekaru 30 yana harkokin kasuwancinsa; kafin daga bisani a naɗa […]

Allah Ya yi wa Malam Bodinga rasuwa

Allah Ya yi wa Malam Abdulmuminu Boɗinga rasuwa a daren Lahadin da ta gabata, inda aka yi masa jana’iza a safiyar Litinin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Marigayin ɗaya ne daga cikin dattawan Kasuwar Mil 12 da ke Legas, inda ya shafe sama da shekaru 30 yana harkokin kasuwancinsa; kafin daga bisani a naɗa shi Alƙali mai yin shari’a da sulhu a ɓangaren ’yan kayan gwari na kasuwar a shekarar 2006; bayan kafuwar kungiyar ’Yan gwari a kasuwar.

Marigayin ya sami kyakyawar shaida daga jama’a da dama. A cewar Alhaji Dauda Tarai, shugaban ɓangaren ’yan tattasai, marigayin mutum ne mai dattaku da ƙwarewa ta fuskar zance; wanda hakan ne ya sanya suka ba shi alƙalanci a kasuwar, inda ya taka gagarumar rawa ta hanyar yin sulhu a tsakanin jama’a a kasuwar.

Marigayin ya rasu bayan ya yi jinya a garinsu na Gidangiwa da ke Boɗinga a Jihar Sakkwato, ya bar ’ya’ya 11 uku maza sai mata takwas.