Allah Ya yi wa Mamman Kankiya rasuwa
A ranar Litinin da ta wuce ne Allah Ya yi wa Alhaji Muhammadu Kankiya wanda aka fi sani da Mamman Kankiya rasuwa, bayan gajeruwar rashin lafiya. Marigayin mai shekara 95, ya rasu ne a gidansa da ke Lamba 1, Titin Marnona a Unguwar Sarkin Musulmi, Kaduna bayan ya yi jinya na mako hudu a asibiti. […]
A ranar Litinin da ta wuce ne Allah Ya yi wa Alhaji Muhammadu Kankiya wanda aka fi sani da Mamman Kankiya rasuwa, bayan gajeruwar rashin lafiya.
Marigayin mai shekara 95, ya rasu ne a gidansa da ke Lamba 1, Titin Marnona a Unguwar Sarkin Musulmi, Kaduna bayan ya yi jinya na mako hudu a asibiti.
Aminiya ta samu labarin cewa marigayi Mamman Kankiya ya rasu ne da misalin karfe 7:00 na safiyar Litinin.
daruruwan mutane ne suka halarce jana’izarsa wanda Dokta Ahmad Abubakar Gumi ya jagoranta a masallacin Sarkin Musulmi Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna da misalin karfi 1:15 na ranar, bayan idar da Sallar Azahar a masallacin.
daya daga cikin ’ya’yan marigayin Malam Wa’ilu Muhammad Kankiya ya bayyana marigayin da mutumin kirki. “Baba mutum ne da ya yarda da bai wa ’ya’yansa da sauran mutane shawarwari a kan yadda za su zauna da mutane da kuma inganta rayuwarsu. Shi ba mutum ba ne da ke dukan yara sai dai ya ba ku shawara idan kuka yi kuskure. Yana son mutane, ya dauki kowane yaro a matsayin dansa. Za mu yi kewarsa, Allah Ya jikansa Ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi,” inji shi.
Marigayi Mamman Kankiya ya rasu ya bar ’ya’ya 11 da mace daya, inda matarsa ta farko ta rasu a shekarar 2000.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci Sallar Jana’izarsa sun hada da Sheikh Muhammadu Sunusi Gumbi da Hakimin Doka da Kwamared Zubairu Shan’una da manyan malamai da dubban Musulmi.