Allah Ya yi wa Maraɗin Katsina rasuwa
Allah Ya yi wa Alhaji Amadu Kurfi, tsohon Sakataren tsohuwar hukumar zaɓe (FEDECO) rasuwa
Allah Ya yi wa Alhaji Amadu Kurfi, tsohon Sakataren tsohuwar hukumar zaɓe (FEDECO) rasuwa.
Alhaji Amadu Kurfi ya rasu ne yana da shakara 90, a daren ranar Laraba bayan ya yi fama da jinya.
A lokacin rayuwarsa, marigayin shi ne Maraɗin Katsina kuma Hakimin Kurfi na farko.
Shi ne kuma ne wanda ya fi kowa yawan shekaru daga cikin hakiman Masarautar Katsina.
Za a yi jana’izarsa ranar Alhamis ɗin nan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.