Sa’in Katsina Alhaji Ahmadu Na Funtuwa ya rasu

Marigayi Alhaji Ahmadu Na Funtuwa shi ne dan majalisar Sarki da ya fi kowa dadewa

Sa’in Katsina Alhaji Ahmadu Na Funtuwa ya rasu

Sa’in Kastina Alhaji Marigayi Amadu Na Funtuwa ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru sama da 90.

Alhaji Marigayi Amadu ya rasu ne a ranar Alhamis a Asibitin Koyarwa ta Tarayya da ke Katsina bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Marigayin shi ne Sa’in Katsina na farko wanda Marigayi Sarkin Katsina, Usman Nagogo ya nada, kuma shi ne dan majalisar Sarki da ya fi kowa dadewa.

Sa’in ya yi zamani da sarakunan Katsina uku, Sa Usman Nagogo, Sarki Kabir Usman Nagogo da kuma Sarki na yanzu Abdulmuminu Kabir.

Marigayin dan uwa ne ga tsohon Sojan nan Abba Siri-siri kuma ya yi tashe a harkokin siyasa tun a zaman da ya yi a kasar Saliyo kafin dawowarsa gida.

Mutun ne mai son ganin ba a yi watsi da harkokin addini da na al’adu ba tare da wasannin motsa jiki.

Daga cikin ’ya’yan da ya bari akwai Alhaji Muntari Sa’i da sauran su gami da jikoki masu yawa

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka