…Allah Ya yi wa Sarkin Gusau rasuwa
Allah Ya yi wa Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau a Jihar Zamfara Alhaji Muhammadu Kabir danbaba rasuwa a jiya Alhamis. Mai martaba Sarkin ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Abuja yana da shekara 91 bayan ya yi jinya.Marigayi Sarki danbaba ya kwashe shekara 31 a bisa karagar mulki.Kamar yadda Kwamishinan Watsa Labarai […]
Allah Ya yi wa Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau a Jihar Zamfara Alhaji Muhammadu Kabir danbaba rasuwa a jiya Alhamis.
Mai martaba Sarkin ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Abuja yana da shekara 91 bayan ya yi jinya.
Marigayi Sarki danbaba ya kwashe shekara 31 a bisa karagar mulki.Kamar yadda Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Zamfara Alhaji Ibrahim Muhammad ya shaida wa BBC ya ce an yi jana’izarsa da misalin karfe 9:00 na dare a Babban Masallacin Gusau.
An haifi Alhaji Muhammadu Kabir danbaba a Gusau, fadar Jihar Zamfara a 1927, marigayin wanda aka shaide shi da dattaku da kyakkyawan hali da mutunci, an nada shi Magajin Garin Gusau a 1974 yana da shekara 47, bayan shekara 10 ne aka nada shi Hakimin Gusau inda ya rike sarautar na shekara 13, inda a 1997 bayan kirkiro Jihar Zamfara aka nada shi Sarkin Gusau kuma Sarki Mai daraja ta Biyu.
A shekara ta 2000 an daga darajar masarautar zuwa Sarki Mai daraja ta daya, matsayin da yake rike da shi har zuwa rasuwarsa.
Sarki Muhammadu Kabir ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya 37.