Allah Ya yi wa Sarkin Ningi rasuwa

Sarkin Ningi ya rasu bayan kwanaki biyu da dawowa daga jinya a Saudiyya.

Allah Ya yi wa Sarkin Ningi rasuwa

Mai Martaba Sarkin Ningi, Dokta Yunusa Muhammadu Dan Yaya OON, ya riga mu gidan gaskiya.

Aminiya ta samu cewa Sarkin ya rasu ne safiyar wannan Lahadin a Jihar Kano.

Sarkin ya rasu ne a Asibitin Expert Alliance da ke Kano, kwanaki biyu bayan dawowa daga tafiyar ganin likita da ya je birnin Makkah na Saudiyya.

Wata sanarwar da Sakataren Fadar Ningi, Alhaji Usman Sule Magayakin Ningi, ta ce za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 4.00 na Yamma a fadar.