Allah ya yi wa Sarkin Sudan na Kontagora rasuwa
Sarkin ya rasu a asibiti a Abuja bayan ya sha fama da jinya.
Allah ya yi wa Sarkin Sudan na Kontagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska rasuwa.
Sarkin ya rasu yana da shekara 84, bayan ya shafe shekara 47 a kan karagar mulkin sarautar Kontagora da ke Jihar Neja.
- Yadda jama’ar gari suka kama dan bindiga da hannu a Katsina
- An jefe ma’akacin gidan talabijin na NTA har lahira
Aminiya ta gano cewa sarkin ya rasu ne a Abuja wani asibiti da ba a bayyana ba.
Sarkin ya rasu ya bar mata, ‘ya’ya da jikiko masu yawa.
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana rashin sarkin a matsayin wata asara da ba za a maye gurbinta ba.
Kazalika, ya bayyana sarkin Kontagora a matsayin mutum mai kaunar wanzuwar zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana cewar za a yi jana’izar sarkin da misalin karfe 4 na yammacin ranar Alhamis, a fadar sarkin Sudan da ke Kontagora, Jihar Neja.