Allah Ya yi wa Sarkin Tafa rasuwa

Allah Ya yi wa Sarkin Tafa da ke karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna Malam Adamu Sulaiman rasuwa. Garin Tafa wanda mahada ne na masu manyan motoci da ke kan iyakar Jihar Kaduna da Neja a hanyar Kaduna zuwa Abuja, an kafa shi ne kimanin shekara 37.Marigayin wanda shi ne Sarkin Tafa na farko ya […]

Allah Ya yi wa Sarkin Tafa rasuwa
Allah Ya yi wa Sarkin Tafa rasuwa

Allah Ya yi wa Sarkin Tafa da ke karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna Malam Adamu Sulaiman rasuwa.

Garin Tafa wanda mahada ne na masu manyan motoci da ke kan iyakar Jihar Kaduna da Neja a hanyar Kaduna zuwa Abuja, an kafa shi ne kimanin shekara 37.
Marigayin wanda shi ne Sarkin Tafa na farko ya rasu ne a ranar Lahadi 22 ga Maris yana da shekara 94.
Ya rasu ya bar ’ya’ya biyar da jikoki 20. Daga cikin ’ya’yansa akwai Dagacin Tafa Malam Nasidi Adamu. Kuma an yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada tun a ranar da ya rasu.