Allah Ya yi wa Sarkin Zango Eyaen Rasuwa

Al’ummar Arewa mazauna zangon Eyaen na Benin Jihar Edo suna jimamin rasuwar marigayi Sarki Alhaji Muhammadu Jingudo, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a makon jiya. Marigayin ya rasu yana da shekaru sittin da biyar a duniya, ya bar matan aure guda biyu da ’ya’ya maza da mata 17 da jikoki 15.Sarkin ya rasu ne […]

Allah Ya yi wa Sarkin Zango Eyaen Rasuwa
Allah Ya yi wa Sarkin Zango Eyaen Rasuwa

Al’ummar Arewa mazauna zangon Eyaen na Benin Jihar Edo suna jimamin rasuwar marigayi Sarki Alhaji Muhammadu Jingudo, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a makon jiya.

Marigayin ya rasu yana da shekaru sittin da biyar a duniya, ya bar matan aure guda biyu da ’ya’ya maza da mata 17 da jikoki 15.
Sarkin ya rasu ne bayan wata gajeruwar jinya a Asibitin Koyarwa (UBTH) da ke Benin Jihar Edo. Wani na hannun damansa, Alhaji Abdulrahman Abubakar Yola ya bayyana wa Aminiya halayyarsa. “A sanina da shi sama da shekara ashirin, marigayin tun daga farko har ya zuwa karshen da mutuwa ta raba mu ba ya da abokin fada, domin mutum ne mai son a zauna lafiya kuma mai kwatanta gaskiya da adalci a cikin shugabancinsa. Yana girmama kowa ko da yaro ne karami idan ya zo da matsalarsa sai ya tsaya ya saurare shi tare da bi masa kadinsa. Don haka sai dai muce Allah ya gafarta masa.” Inji shi.
Tuni dai aka yi jana’izar mamacin a garin Benin bisa tsarin addinin Musulunci, tare da addu’ar Allah Ya jikansa.