Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa

Ɗan malamin, Sayyadi Ali ne ya tabbatar da rasuwar mahaifin nasa.

Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa

Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musulunci nan daga Jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu.

Ɗansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ne,  ya tabbatar wa Aminiya rasuwar malamin.

Ya ce sun karɓi wannan ƙaddara tare da gode wa Allah bisa rayuwar da malamin ya yi.

“Tabbas Sheikh ya koma ga Mahaliccinsa. Daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma,” in ji Sayyadi.

“Lokacin Sheikh ya yi. Mun gode wa Allah Maɗaukaki. Ya bai wa Sheikh tsawon rai, kuma rayuwarsa ta yi kyau. Alhamdulillah,” in ji shi.

Rahotanni sun bayyana cewar jikin malamin ya tashi a ranar Laraba, inda aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na ATBU, inda ya rasu da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Marigayin ya rasu yana da shekara 101 a duniya.

Za a yi jana’izar Dahiru Bauchi a gidansa da ke kan titin zuwa Gombe a ranar Juma’a.