Allah Ya yi wa Sheikh Giro Argungu rasuwa

Shugaban Izala na kasa, Sheikh Bala Kau ne ya sanar da haka

Allah Ya yi wa Sheikh Giro Argungu rasuwa

Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Abubakar Giro Argungu rasuwa.

Malamin dan asalin Jihar Kebbi ya rasu ne a daren Talata, bayan fama da jinya a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.

Shugaban kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya sanar da haka a cikin wani sako da ya wallafa a shafi da na Facebook da maraicen Laraba.

Sheikh Bala Lau, “Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji’un. Allah Ya yiwa Sheikh Abubakar Giro Argungu Rasuwa.

“Marigayin ya rasu ne bayan jinya da ya yi na dan lokaci a Birnin Kebbi.

“Za a gabatar da sallar janazan marigayi Sheikh Abubakar Giro da misalin karfe biyu na rana (2:00pm), a masallacin Idin Sarki da ke garin Argungu a Jihar Kebbi, Najeriya Insha Allah,” in ji shugaban na Izala.

Marigayin dai fitaccen malamin addinin Musulunci ne a ke wa’azi a cikin da wajen Najeriya da ma makwabtan kasashe irin su Jamhuriyar Nijar da Ghana da Kamaru da Chadi da kuma Benin.

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024