Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa

Malamin ya rasu bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci nan na Jihar Kaduna, Sheikh Ishaq Yunus Almadany, ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Ya rasu a ranar Alhamis a Asibitin 44 Army Reference da ke Kaduna.

Jami’in hulɗa da jama’a na na kafafen sada zumunta na ƙungiyar Izalatul Bidia Waikamatus Sunnah (JIBWIS), Ibrahim Shehu Giwa ne, ya tabbatar da rasuwar.

Shugaban JIBWIS reshen Jihar Kaduna, Alhaji Adamu Ibrahim, ya bayyana alhininsa, tare da yin addu’ar Allah Ya gafarta masa Ya kuma Aljanna makomarsa.

Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, shi ma ya sanar da rasuwar malamin a shafinsu na Facebook, inda suka yi addu’ar Allah Ya jiƙansa.

Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5 na yamma a filin idi na Sultan Bello, da ke Kaduna.

Malamai sun fara yajin aiki a Ebonyi

Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibai

Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa

An tsinci gawar Ɗan Majalisar da aka yi garkuwa a jajibirin Kirsimeti