Allah Ya yi wa Yariman masarautar Zazzau rasuwa

Marigayin ya rasu ya bar ‘ya’ya da mata da dama.

Allah Ya yi wa Yariman masarautar Zazzau rasuwa

Allah Ya yi wa Yariman Masarautar Zazzau kuma Hakimin Ikara, Injiniya Aminu Umar rasuwa.

Hakimin, ya rasu ne bayan ya halarci bukukuwan sallah da masarautar ta gudanar.

Marigayin wanda shi ne Hakimin Ikara, ya fito ne daga zuri’ar marigayi Sarki Dalhat daga gidan Barebari a masarautar Zazzau.

Ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Hukumar Ruwa ta Jihar Kaduna.

Marigayin wanda ke riƙe da sarautar Walin Zazzau, yana ɗaya daga cikin masu riƙe da manyan mukamai a masarautar.

Shugaban sashen yada labaran masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce marigayin ya halarci Hawan Daushe da aka yi, kuma yana ɗaya daga cikin hakiman da suka gaishe da Sarkin Zazzau Malam Mallam Ahmed Nuhu Bamalli.

Marigayi Walin Zazzau ya rasu ya bar mata da ’ya’ya da dama.

Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a yankin Amaru da ke Zariya.

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi

Ɗan shekara 85 ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe

Yadda muke rayuwa bayan mutuwar mazajenmu —Matan sojoji