Allegri zai sake komawa Juventus

Massimilano Allegri zai sake komawa Juventus a karo na biyu.

Allegri zai sake komawa Juventus

Massimilano Allegri

Rahotannin daga Italiya sun nuna tsohon kocin Juventus, Massimilano Allegri, ya amince zai koma kungiyar don maye gurbin Andre Pirlo.

Allegri ya ajiye aikin horar da Juventus a 2019, inda kungiyar ta dauki Maurizio Sarri.

Sarri ya shafe kakar wasa daya da Juventus, amma daga karshe suka raba gari, kungiyar ta dauki tsohon dan wasanta Andre Pirlo a matsayin sabon kocinta a 2020.

Sai dai Juventus ta sha fadi-tashi a karkashin Pirlo, har ta yi rashin nasarar lashe gasar Seria A a karon farko tun bayan shekaru tara.

Tuni aka shiga yada rade-radin cewar kungiyar za ta sallami Pirlo tare da neman sabon mai horarwa.