Allurar Foliyo: dangote zai fara bayar da kyauta ga iyayen yara

Shugaban Rukunin Kamfanonin dangote, Alhaji Aliko dangote ya bullo da shirin bayar da kyauta ga iyayen da suka yarda aka yi wa ’ya’yansu allurar rigakafi a matsayin karfafa gwiwa ga mazauna karakara da ke kananan hukumomin 44 na Jihar Kano su amince da allurar rigakafin shan inna da ake yi lokaci-lokaci.Alhaji Aliko ya yi wannan […]

Allurar Foliyo: dangote zai fara bayar da kyauta ga iyayen yara

Alhaji Aliko Dangote

Alhaji Aliko DangoteShugaban Rukunin Kamfanonin dangote, Alhaji Aliko dangote ya bullo da shirin bayar da kyauta ga iyayen da suka yarda aka yi wa ’ya’yansu allurar rigakafi a matsayin karfafa gwiwa ga mazauna karakara da ke kananan hukumomin 44 na Jihar Kano su amince da allurar rigakafin shan inna da ake yi lokaci-lokaci.
Alhaji Aliko ya yi wannan alkawari ne a wani taron rabin shekara da aka yi a karshen makon jiya a Kano, inda ya ce akwai bukatar bullo da wani shiri na bayar da sakamako da kuma ladabtarwa don a kori wanann cuta daga jihar.
Ya ce daga yanzu duk matar da ta bayar da danta aka yi masa allurar rigakafin shan inna za a ba ta kyautar kayan kamfanin dangote da suka hada da taliya da sukari da sauransu.
Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya Kamfanin dangote da Asusun Bill &Melinda Gates da kuma Gwamnatin Jihar Kano suka hada hannu don nemo hanyoyin yaki da cutar shan inna a jihar. Daga cikin hanyoyin akwai bayar da karfi a kan abin da ya shafi rigakafi.
A lokacin da yake jawabi a wurin taron Shugaban Asusun Bill &Melinda Gates, Mista Bill Gates ya ce ya ji dadin bayanan da ya samu game da shirin, don haka ya kuduri aniyar kara bayar da gudunmawa don ganin shirin ya kai ga nasara.
A jawabin Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce shirin yana samun tagomashi daga bangaren gwamnati domin ganin ya samu nasara, haka kuma kokarin bangarorin ya taimaka wajen samun kyakkyawan sakamako, kasancewar a yanzu fiye da kashi uku daga cikin 28 a shekarar 2012 na cutar ya ragu.
Sannan ya ce za a rika saka wa duk karamar hukumar da ta yi fice wajen aiwatar da rigakafin don a karfafa gwiwar sauran kananan hukumomin jihar. 

…Sarkin Yawuri ya shawarci jama’arsa kan allurar

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

Mai martaba Sarkin Yawuri a Jihar Kebbi Dokta Muhammadu Zayyanu Abdullahi ya shawarci magidanta da ke masarautarsa su daure wajen fitar da ’ya’yansu don a diga musu maganin cutar poliyo a duk lokacin da jami’an rigakafin suka je gidajensu.
Sarkin ya ba da wannan shawarar ce a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan allurar poliyo a fadarsa da ke Yawuri, inda ya ce babu wata matsala a tattare da allurar cutar shan-inna, kuma rashin yin ta babbar barazana ce ga lafiyar yaranmu, “masu adawa da allurar su sani cewa ba da Najeriya kadai suke yi ba da likitocin duniya ne baki daya,” inji Sarkin.
Sarkin ya kara jawo hankalin magidanta su rika sanya iyalansu suna tsabtace muhallansu tun daga cikin dakunansu da filin gida da kofar gida da kuma jikinsu, kuma su rika tura mata masu juna biyu suna zuwa asibiti domin awo, sannan idan suka haihu su kai ’ya’yansu a yi musu dukkan alluran da suka dace.
Sarkin ya kuma umarci hikimai da dagatai da masu unguwanni su rika fita tare don shawo kan mutanen da ba su bayar da da hadin kai ga allurar rigakfin, inda ya roki iyaye maza da mata su bayar da hadin kai ga shirin domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Da yake zantawa da Aminiya shugaban kwamitin wayar da kan jama’a kan yaki da cutar shan-inna a masarautar Yawuri Alhaji Muhammad Bawa, ya ce malamai da limamai suna da gudunmawar da zu ba da wajen jawo hanlakin mutane a cikin wa’azi da hudubobin da suke gabatarwa don a samu nasarar shirin. Shugaban ya ce idan akwai illa a cikin allurar ba za su kai wa mutanensu ba.