Almajira ta rasu ta bar Naira miliyan 124
Wata almajira da ta shafe shekaru da dama tana bara a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, ta rasu ta bar dukiya kimanin Riyal miliyan 3 (kwatankwacin Naira miliyan 124).Dattijuwar mai suna A’isha ta rasu tana da shekaru 100 ne, kuma cikin kadarorin da ta bari har da rukunin gidaje da kuma zinare mai yawa. Cikin […]
Wata almajira da ta shafe shekaru da dama tana bara a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, ta rasu ta bar dukiya kimanin Riyal miliyan 3 (kwatankwacin Naira miliyan 124).
Dattijuwar mai suna A’isha ta rasu tana da shekaru 100 ne, kuma cikin kadarorin da ta bari har da rukunin gidaje da kuma zinare mai yawa.
Cikin wadanda ke mamakin dukiyarta har da ’yan hayan da ke zaune a cikin gidajen da ta bari, wadanda suka ce da ma su sun kasa gane dalilin da ya sa shekara da shekaru ba sa fuskantar karin kudin haya.
Wani wanda ya kula mata da dukiyar, mai suna Ahmad al-Saeedi ya ce hukumomin Saudiyya sun karbe dukkan dukiyar da ta bari, sai dai bai da masaniyar ko za su tashi ’yan hayan da ke haya a gidajenta.
Ya kara da cewa akasarin abun da ta bari ta tara ne a lokacin da suke bara tare da mahaifiyarta da kuma wata kanwarta. Bayan rasuwarsu ne ta ci gadon dukiyar ita kadai.
Ahmad ya kuma bayyana cewa mabaratan sukan samu goma ta arziki na sadaka ne saboda yadda jama’a ke musu kallo wadanda ya dace a taimaka musu.
Ya ce akwai lokuta da dama da ya yi iya kokarinsa don ganin ya hana A’isha yin barace-barace saboda ganin irin dukiyar da ta mallaka, amma sai ta yi kememe, ta ki.