Almajirai 193 sun kamu da coronavirus a Kano

Gwamnatin Kano ta ce almajirai 193 sun kamu da cutar coronavirus a jihar, lamarin da ya haifar da damuwa game da mayar da almajirai jihohinsu. Da yake bayani game da rufe makarantun allo a fadin jihar, Kwamishinan ilimi Sunusi Muhammad Kiru, ya ce an kwashe akalla almajirai 1,500 daga jihar Kano zuwa jihohinsu, ita kuma […]

Almajirai 193 sun kamu da coronavirus a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin Kano ta ce almajirai 193 sun kamu da cutar coronavirus a jihar, lamarin da ya haifar da damuwa game da mayar da almajirai jihohinsu.

Da yake bayani game da rufe makarantun allo a fadin jihar, Kwamishinan ilimi Sunusi Muhammad Kiru, ya ce an kwashe akalla almajirai 1,500 daga jihar Kano zuwa jihohinsu, ita kuma aka dawo mata da guda 400.

Kwamishinan ya ce, “Lokaci ya wuce na alarammomi su rika kwaso almajirai da ba su ma san inda almajiran suke kwana ba”, don haka wajibi ne duk mai son bude makarantar allo a jihar ya samar da dakunan kwanan almajirai.

Hakan na zuwa ne lokacin da gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya cire dokar kulle a fadin jihar face daga 10.00 na dare zuwa 4.00 na asuba.

Da yake jawabi, shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar Kano, Dakta Tijjani Hussain, ya ce mutum daya ne aka samu yana dauke da kwayar cutar daga cikin mutum 2,000 da aka yi wa gwaji na gida-gida a Karamar Hukumar Nassarwa.

A cewarsa hakan ya saba da rahoton hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) da ya ambato karamar hukumar a jerin sunayen warare da cutar ta fi kamari a Najeriya.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno