Almajirai sun tsinci jariri a Kaduna
Wasu almajirai sun tsinci jaririn da aka yada a kan titin Race Course da ke daura da Dandalin wasa na Multara da ke Kaduna. Al’amarin ya auku ne a makon da ya wuce lokacin da almajiran ke kan hanyarsu ta zuwa bara.A cewarsu, sun baro makarantar allonsu ne da ke Unguwar Sanusi a kan hanyarsu […]
Wasu almajirai sun tsinci jaririn da aka yada a kan titin Race Course da ke daura da Dandalin wasa na Multara da ke Kaduna.
Al’amarin ya auku ne a makon da ya wuce lokacin da almajiran ke kan hanyarsu ta zuwa bara.
A cewarsu, sun baro makarantar allonsu ne da ke Unguwar Sanusi a kan hanyarsu ta zuwa bara sai suka hangi leda a cikin wani kwalbati. Sun ce da suka matsa kusa domin ganin abin da ke cikin ledar sai suka ji kukan jariri.
Ganin hakan ne a cewar shaidun gani da ido sai yaran suka yi kuwwa wanda hakan ya jawo hankalin jama’a suka matsa inda yaran suke domin ganin abin da suke yi wa ihu.
Wata ’yar jarida mai suna Amina Amobi wacce abin ya faru a kan idonta ta shaida wa Aminiya cewa a lokacin ta zo wucewa ne ta ga an taru sai ta matsa domin ganin abin da ke faruwa. “Koda na matsa kusa sai na ga almajiran sun kewaye leda, kuma ganin babu wanda ya bude ledar daga cikinsu kuma ga kukan jariri sai na daure na bude ledar. Bude ta ke da wuya sai ga jariri sabon haihuwa har an yanke masa cibiya.Wannan abu ya yi matukar tada hankalina,” inji ta.
Ta bayyana cewa saboda ganin jaririn ba ya sanye da kaya sai da ta dauki zanenta nan take da lullube shi.
Haka kuma ta ce wasu mata da suka iso wurin sun taimaka wajen dumama jaririn saboda tausayi.
Ta ce daga bisani an kira ’yan sanda wadanda suka dauke shi zuwa ofishinsu domin ci gaba da kula da shi.