Almajiran Abduljabbar na roko a bude masallacinsa

Sun bukaci a yi mukabala tsakaninsa da malaman Kano don gaskiya ta yi halinta

Almajiran Abduljabbar na roko a bude masallacinsa

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Daliban Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda Gwamnatin Kano ta dakatar daga gudanar da majalisi ta kuma rufe masallacinsa, na rokon ta ta bude masallacin tunda watan Azumin Ramadan ya zo.

Sun kuma bukaci gwamnatin ta shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da malaman jihar da ke zargin sa da cin mutumin magabata na gari da kuma neman tayar da fitina, domin gaskiya ta yi halinta a sabanin da ke tsakanin bangarorin.

“Mu mabiyansa da almajiransa muna rokon Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya sa sake bude majalisin da masallacin da aka rufe saboda al’ummar Musulmi su fa’idantu,” inji su.

Almajiran sun yi rokon ne a wani taron ’yan jarida a Kaduna, inda suka koka cewa an yi watanni da rufe masallacin malamin nasu bayan takaddamar da aka samu tsakaninsa da malaman.

Kakakin almajiran na Abduljabbar, Imam Mohammed Rabiu Zakariya, ya musanta zargin da ake wa malamin, yana mai cewa babu wani malamin addini a Najeriya da ya fi shi son zaman lafiya.

Ya kara da cewa Shaikh Abduljabbar bai taba yin batanci ga Manzon Allah (SAW) ba kuma ba zai taba yi ba.

Game da zargin da ake wa malamin da zama mabiyin akidar Shi’a, Imam Zakariya ya ce malamin nasu ba ya nuna bambanci tsakanin Musulumai kuma yana mutunta kowannensu.

Ya ce masu halartsar darussan da Shaikh Abduljabbar yake gabatarwa sun hada da mabiya darikar Tijjaniya, Shi’a, Kadiriyya har ma da ’yan Izala.

Don haka ya yi kira ga malaman da fahimtarsu ta saba da na Abduljabbar da su daina zubar masa da mutunci.