Almajiranci irin na Kirista (1)

Bisa ga yardar Ubangiji Allah; a yau za mu fara nazari a kan wannan magana – wato almajiranci. Almajiranci abu ne mai muhimmanci a cikin rayuwar kowane Kirista, a yau mutane da yawa cikin Ekklisiyar Almasihu sun yi watsi da wannan shiri da Ubangijinmu Yesu Kiristi ya koya mana mu yi: a cikin Littafin Matta […]

Almajiranci irin na Kirista (1)
Almajiranci irin na Kirista (1)

Bisa ga yardar Ubangiji Allah; a yau za mu fara nazari a kan wannan magana – wato almajiranci. Almajiranci abu ne mai muhimmanci a cikin rayuwar kowane Kirista, a yau mutane da yawa cikin Ekklisiyar Almasihu sun yi watsi da wannan shiri da Ubangijinmu Yesu Kiristi ya koya mana mu yi: a cikin Littafin Matta 28:18–20, Yesu Kiristi ya yi magana da almajiransa bayan mutuwarsa da kuma tashinsa daga kabari – “Yesu kuwa ya zo wurinsu, ya yi zance da su, ya ce, Dukan hukunci a cikin sama da kasa an bayar gare ni. Ku tafi fa, ku almajirtar da dukan al’ummai, kuna yi musu baptisma zuwa cikin sunan Uba da na da da na Ruhu Mai tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umarce ku: ga shi kuwa ina tare da ku kullum har matukar zamani.” 

Abu na farko da nake so mu gane sosai shi ne almajirtar da mutane, ba ra’ayin mutum ba ne. Umarnin Yesu Kiristi da kansa ne; domin haka akwai muhimmancin sanin yadda za a yi aiki bisa ka’idar da akwai bisa ga koyarwar Ubangiji Allah. Masu bin Yesu Kiristi da dama ba su san mene ne almajiranci ba sosai; shi ya sa akwai bukata sosai cikin ekklisiya na mutane wadanda suke da tushe da suka kafu sosai cikin sanin wannan bangaskiyar da muke da ita cikin Ubangiji. Abu mafi muhimmanci cikin rayuwar kowane mai bin Yesu Kiristi shi ne; mu nuna rayuwar Kiristi a cikin namu kuma mu almajiranttar da mutane da suke karkashinmu domin su ma su dauki kamaninsa.
Wannan aiki dole ne mu yi shi da kwazo sosai, maganar Allah ta wurin Manzo Bulus, cikin littaffin Kolosiyawa:1:28-29 “… wanda muke shela, muna gargadar da kowane mutum, muna koya wa kowane mutum cikin dukan hikima, domin mu mika kowane kamili cikin Kiristi; da nufin wannan fa nake aiki, ina kwazo bisa ga aiki nasa, wanda ke aikawa cikina da iko.” Wannan shi ne muhimmin aiki da Allah Ya bar mana domin mu yi. Ashe kuskure ne a gare mu idan har ba mu dauki wannan umarni da gaske ba.

Mene ne almajiranci irin na Kirista?:
Almajiranci dai hanyar dasawa ne; ko kuma haifar da rayuwar malami a cikin dalibi. Wannan shiri ne wanda za a bi daya bisa daya har ya sa wani mutum – misali dan makaranta, dalibi, mai koyo, mai neman sani; da sauransu, ya dauki kamanni ko kuma a kamanta shi da surarsa, kamanni da cikakken sifar malamin – a nan muna nufin Ubnagiji Yesu Almasihu. Idan wani ya gan ka a waje; wani irin kamanni ne zai gani a cikinka? Za a iya bambamta ka da sauran wadanda ba su san Yesu Kiristi ba?
Almajiranci, shi ne horarwa na iyalin Allah:- a cikin Littaffin Galatiyawa 4:1–2, maganar na cewa “Abin da nake cewa ke nan, muddar magaji yana da kuruciya, ba inda ya rabu da bawa ba, kodayake shi ubangijin duka; amma yana hannun marika da wakilai har matukar kwanakin da uban ya sanya.” Haka kuma a cikin Littaffin Ibraniyawa 12:7-11, maganar Ubangiji Allah na ce mana, “Domin horo ne kuna jimrewa, Allah Yana yi da ku kamar da ’ya’ya, gama ina dan wanda ubansa ba ya yi masa horo ba? Amma idan kun zama marasa horo, abin da an sa kowa ya karbi rabonsa, shegu ne ku, ba ’ya’ya ba ne. Ban da wannan kuma, muna da ubaninnmu na wajen jiki masu yi mana horo, muka kuwa ba su girma: balle fa mu sarayar da kanmu ga uban ruhohinmu, mu rayu? Gama hakika su suka yi musu horo ’yan kwanaki kadan yadda suka ga dama, amma shi domin amfaninmu, domin mu zama masu tarayya cikin tsarki nasa.kowane irin horo ana ganinsa ba abin faranta zuciya ba ne, amma abin ciwo ne a lokacin da a loton yi: amma daga baya yakan ba da amfani mai salama – wato na adalci ke nan ga wadanda sun watsu ta wurinsa.”
Idan magaji yaro ne, ba za a taba daukar dukiyar da ubansa ya bari dominsa a sa cikin hannunsa ba, yawancin lokaci; iyaye sukan yi shiri da wadansu mutane musamman aminai wacanda suka yarda da su, sai su sa wannan magaji a hannunsu da dukan dukiyarsa, su ba su umarni cewa idan wannan yaron ya kai yawan shekaru kamar haka sai ku damka masa gadon nan nasa. Dole ne kafin magaji yaro ya shigo cikin gadonsa, a sa shi a hannun iyayen goyo da wakilai har ya girma ya gaji ubansa. Wannan ya kunshi horo da gyaran hali. A yau, cikin matsayinmu na masu bi, iyayen goyo da wakilai na mulkin Allah su ne mutane maza da mata da Allah Ya sanya domin su lura da girma da ci gabanmu har mu zama kamar kaunatattun ’ya’yansu. Wannan shi ne almajiranci; duk wanda ya ki wannan horarwa na iyalin masu bin Yesu Kiristi, shi ne ya taurare, ya kuma zama shege bisa ga littafi, mai yawon banza. Irin wannan mutum ba zai taba shiga cikin ainihin gadon da Ubangiji Allah Ya bar mana ba. Horo ba abu ne mai sauki ba ko kadan, wani lokaci akwai zafi; amma idan mun jure har zuwa karshe, za mu shiga cikin gadon da Allah Yake mana cikin Yesu Kiristi. Akwai alkawurai da yawa da Allah Ya yi wa masu binsa cikin Littafi Mai tsarki, amma yawancin masu bi, ba su shiga wancan matsayin ba har yanzu; ba domin komai ba sai domin sun kasa su yi koyi da Rayuwar Yesu Kiristi yayin da yake cikin duniya. Idan har muna son mu iya yin abin da Yesu Kiristi ya yi, dole ne mu kawo kanmu karkashin iyayenmu, musamman na ruhaniya, domin su goye mu cikin ruhu su kuma horar da mu domin mu samu mu yi rayuwa mai albarka a wannan duniya. A cikin Littafin Afisawa 4: 11 – 14 maganar Allah na nuna mana dalilin da ya sa baiwa daban-daban cikin EkklisiyarSa “Ya kuma bada wadansu su zama Manzanni, wadansu Annabawa; wadansu masu wa’azin bishara; wadansu makiyaya da masu koyarwa; domin kammalawar tsarkaka, domin aikin hidima, domin ginin jikin Kiristi; har dukanmu mu kai zuwa dayantuwar imani da sanin dan Allah zuwa cikakken mutum, zuwa misalin tsawon cikar Kiristi. Kada nan gaba mu zama yara, wadanda ana wofantar da su suna shillo ga kowace iskar sanarwa, ta wurin wawa – idon mutane masu gwaninta zuwa makidar sabo.” Inda Ubangiji Allah Yake so mu girma mu kai, shi ne misalin tsawon cikar Kiristi. Bari wannan ya zama shi ne abin da zai bishe mu cikin rayuwa ta yau da kullum. Za mu ci gaba idan Allah Ya bar mu a cikin masu rai.
Kada mu manta da ci gaba da yin addu’a domin kasarmu musamman a wannan lokaci na siyasa, Allah Ya zaba mana wanda ya dace da nufinSa, amin.