Almajiranci irin na Kirista (6)
Wane ne almajiri? Makonnin da suka gabata, mun yi ta bincike a kan mene ne almaijiranci; to a yau za mu ci gaba da yin nazari a kan ko wane ne almajiri, akwai masu bin Yesu Kiristi da dama cikin ekklesiya; amma gaskiyar ita ce, da yawa a cikinsu ba almajiran Yesu Kiristi ba ne. […]
Wane ne almajiri?
Makonnin da suka gabata, mun yi ta bincike a kan mene ne almaijiranci; to a yau za mu ci gaba da yin nazari a kan ko wane ne almajiri, akwai masu bin Yesu Kiristi da dama cikin ekklesiya; amma gaskiyar ita ce, da yawa a cikinsu ba almajiran Yesu Kiristi ba ne. Ubangijinmu Yesu Kiristi ya ce, ba duk wanda yake cewa Ubangiji, Ubangiji, ne zai shiga Mulkin Allah ba; sai shi mai aika nufinSa. Akwai mafarin zama almajiri; a cikin Littafin Yohanna 3:3 – 6, maganar Allah na cewa “Yesu ya amsa, ya ce masa, hakika hakika ina ce maka, in ba a haifi mutum daga bisa ba, ba shi da iko shi ga mulkin Allah ba. Nikodimus ya ce masa, kaka za shi yiwu a haifi mutum sa’anda ya rigaya ya tsufa? Ya iya ya sake shiga a cikin cikin uwatasa a haife shi kuma? Yesu ya amsa, ya ce, Hakika, hakika, ina ce maka, in ba a haifi mutum daga cikin ruwa da ruhu kuma, ba shi da iko shi shiga cikin mulkin Allah ba. Abin da an haifa daga cikin nama, nama ne, abin da an haifa daga cikin Ruhu, ruhu ne.” “Amma wannan nake fadi, ’yan uwa, nama da jini ba su da iko su gaji mulkin Allah ba.” (1Korinthiyawa 15:50). “Haka nan a cikin Littafin 1Korinthiyawa 2:14 – Maganar Allah na koya mana cewa “Mutum mai tabi’ar jiki ba shi karbar al’amura na Ruhun Allah ba; gama wauta suke a gare shi; ba shi kuwa da iko ya san su gama ana gwada su cikin ruhaniya.”
Dole ne mu gane abu guda mai muhimmanci, wannan kuwa shi ne, idan ba a sake haifar mutum ta wurin Ruhu Mai tsarki ba, ba shi da ikon kamantuwa da Yesu Kiristi. Babu yadda mutum mai zunubi zai samu horarwa bisa ga dukan tsarin almajiranci wanda zai iya kawo shi ga matsayin tsarkakakken mutum ko yaya ka yi da shi, mai zunubi; mai zunubi ne, babu yadda za ka yi da shi ne, sai har ran da ya samu sabuwar haihuwa cikin ruhu; bari mu dubi misali kamar haka: babu yadda za ka dauki kadangare misali ka horar da shi, ka ciyar da da wannan kadangaren har ya zama akuya nan gaba; ba zai taba faruwa ba ne. Haka nan take; cewa koda an kawo duk tsari na tsari na almajiranci mai zunubi ba zai iya yin girma har ya zama ya tsarkaka ta wurin horarwa ba; dole ne a yanke tsohuwar rayuwarsa, sa’annan a ba shi sabuwar rayuwa. Sabuwar tabi’a, Yesu Kiristi ya yi magana ya ce abin da nama ya haifa, nama ne zai kasance kuma haka zai ci gaba da kasancewa komai irin horarwa da za ka yi. Mutum wanda iyaye na jiki suka haifa, haka zai ci gaba da zama mutum cikin jiki; Amma abin da Ruhun Allah ya haifa ruhu ne. Haka kuma bisa ga maganar Yesu Kiristi; mutum mai tabi’ar jiki, ba shi da iko shi gani balle shiga cikin mulkin Allah; dalilin kuwa shi ne: zuciyarsa ta tabi’ar jiki ne, kuma irin wannan zuciya ba ta da ikon sanin abubuwa ta ruhaniya, a gare shi wauta ne kawai.
Mutum wanda ba a sake haihuwarsa ta biyu ba: wato haihuwa ta wurin Ruhu, ba shi da ikon karbar maganar Allah; kuma ba zai iya faranta wa Allah zuciya ba. Idan har mutum ya samu saduwa da ikon Allah har ya samu ceto, shi kadai ne ke da ikon yin girma da kuma daukar kamanin Yesu Kiristi daga karshe. Irin wadannan mutane ne za su iya zama almajiran Yesu Kiristi su ne za a yi masu horo domin su zama kamar shi kansa da zarar mutum ya karbi Yesu Kiristi ya zama mai cetonsa, yana nan kamar karamin jariri ne wanda dole a shayar da da shi da mama, ya girma har ya zama cikakken mutum. Ko mene ne a jikin babban mutum akwai shi a cikin jariri ma. Sai mu gane da wannan sosai cewa dukan iri na kamantuwa da surar Yesu Almasihu yana cikin duk wanda ya rigaya ya karbe shi a matsayin mai cetonsa. Yesu Kiristi ya yi magana a cikin Littafin Yohanna 8:34 cewa “Hakika Hakika ina ce maku; wanda yana aika zunubi bawan zunubi ne.”
Tambaya ta farko ita ce, kai mai karatu, ko kana aikata zunubi? A wurin da muka yi karatu Ubangijinmu Yesu Kiristi yana cewa; idan kana aikata zunubi, to kai bawan zunubi ne. Mu dubi misali kawai, ko kana karya? Ko kuwa naka fasikanci da zina ne? Ko kana riko a zuci? Ko kana handama? Ko naka zalunci ne? Ko kai mai fahariya ne? Ko kai mai kisan kai ne? Ko kuwa kana aikata irin wadannan abubuwa – kai bawan zunubi ne. Zunubi shi ne maigidanka. Gaskiyar ita ce, idan aka ce da kai bawa, ma’anarta ita ce ba ka da‘yancin yin abin da ka ga dama. Mu duba cikin Littafin Romawa 1: 28 – 32, maganar Allah na cewa “Kuma kamar yadda ba su lamunta su rike Allah a cikin saninsu ba, Allah ya yashe su zuwa ga sangartaccen hankali, da za su aika al’amuran da ba su dace ba, cikakku ne su da dukan rashin adalci, mugunta, kyashi, keta, cike da kishi; kisan kai; husuma, makirci, bakin hali, masu annamimanci, masu kire, abin ki ga Allah, masu tsaurin ido, masu alfarma, masu ruba, masu cira munanan ayyuka, masu kin bin iyaye, marasa azanci, masu tada alkawari, marasa kauna irin ta tabi’a, marasa jinkai, wadanda sun san hukuncin Allah cewa, masu aikata wadannan abu sun isa mutuwa, duk da haka ba aikatawa kadai suke yi ba, amma gama baki suke yi da masu aikatawa.”
Idan har kana karkashin irin wannan zunubi ko kuwa watakila ma za a iya cewa zunubai, ka sani fa ba ka da ’yancin kanka ko kadan; kuma ba za ka taba zama almajirin Yesu Kiristi ba. Kamar yadda muka yi magana; zunubi shi ne maigidanka kuma ba ka da iko ka ki umarnin maigidanka domin bawa; ba shi da damar yin haka. Shi zunubin nan, shi ke mallakar rayuwarka.
Idan kuwa har kana son ka zama almajirin Yesu Kiristi dole sai wani abu ya faru da rayuwarka tukuna. Za mu so mu ci gaba da wannan bincike mako mai zuwa idan Mai duka Ya bar cikin masu rai. Ubangiji ya taimake mu mu samu cikakken fahimi da ganewa; mu kuma iya rayuwa wadda za ta gamshi Ubangiji Allahnmu.
Kada mu manta cin gaba da yin addu’a domin wannan kasar tamu mai albarka, musamman ma a wannan lokaci na siyasa. Allah Ya ba mu zaman lafiya, amin.