Almajiranci irin na Kirista (8)
Wane ne almajiri?: Makon da ya shige, mun soma koyarwa ne a kan ko wane ne almajiri; za mu ci gaba da wannan bincike domin mu iya ganewa, mu kuma iya tambayar kanmu ko mu din nan almajirai ne ko kuwa muna tsammani watakila mu almajirai ne; akwai mutane da dama kamar haka wadanda suna […]
Wane ne almajiri?:
Makon da ya shige, mun soma koyarwa ne a kan ko wane ne almajiri; za mu ci gaba da wannan bincike domin mu iya ganewa, mu kuma iya tambayar kanmu ko mu din nan almajirai ne ko kuwa muna tsammani watakila mu almajirai ne; akwai mutane da dama kamar haka wadanda suna tsammani ne, domin ba su da tabbaci cikin zuciyarsu cewa sun rigaya sun sami ceto ta wurin ban-gaskiya cikin Yesu Kiristi. Mun riga mun gani cikin maganar Allah cewa, “…. dukan wanda yana aikata zunubi bawan zunubi ne.” Wato; maigidan irin wannan mutum mai aikata zunubi, Shaidan ne da kansa. Irin wannan mutum ba ya da iko ya ki yin zunubi cikin rayuwarsa, dole ne ya aikata nufin maigidansa, duk mutumen da har yanzu yake zaune cikin zunubi domin bai karbi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsa ba, ba almajirin Yesu ba ne. Irin wannan mutum, ba ya da iko ya ki yin zunubi, za ka ci gaba da aikata zunubi koda ba ka so. Wani abu zai yi ta iza ka cikin wannan ko kuwa wancan zunubi ba tare da sonka ba. Yawancin lokaci maimakon ka juyo ka tuba ka kuma bar irin wadannan miyagun ayyuka, sai ka yi ta ba da hujjoji, wani lokaci ma sai ka ce ruhu yana da niyya amma jiki rarraunne ne; wannan ba hujja ba ce ko kadan, gaskiyar ita ce zunubi ya rigaya ya mallaki zuciyarka, ba ka da ’yanci ka ce a’a da yake zunubi ya riga ya mallake zuciyarka; kuma zunubin ne maigidanka.
Almajiri mutum ne wanda ya fi karfin zunubi, yana da iko a kan zunubi da Shaidan da kansa. Wannan kuwa shi ne dalilin zuwan Yesu Kiristi cikin wannan duniya. A cikin Littafin Matta 1: 21, maganar Allah ta ce: “Kuma za ka kira sunansa Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” Yesu Kiristi ya zo duniya domin ya ci nasara a kan zunubi a madadinka. Duk lokacin da mutum ya sadu da Ubangiji, abu na farko da Allah Yake yi shi ne maganta zunubi. Rabuwa da rashin adilci, kuma a kafa tushe mai karfi cikin tafiya da Allah. Maganar Allah na koya mana cewa “Amma tushe mai tsayawa na Allah ya tabbata, da yake yana da wannan hatimi, Ubangiji ya san wadanda ke nasa da kuma, dukkan wanda ya ambaci sunan Ubangiji ya rabu da rashin adalci.” 2Timothawus 2: 19. Haka nan kuma cikin Littafin Yohanna 8: 36, maganar Allah na cewa: “Idan fa dan za ya yantar da ku, ku zama ’yantattu da gaske.” Mu lura sosai da wannan; cewa Yesu Kiristi ne shi kadai zai iya ’yantar da kai daga bautar zunubi; har ka iya samun ’yanci na bauta wa Allah cikin tsarki da adalci dukan kwanakin ranka; har sai wannan ya faru; wato saduwa da Yesu Kiristi sa’annan tabi’ar Almasihu, iko na kamantuwa da shi zai shigo cikin rayuwarka. Babu wata hanya kuma. Irin wannan mutum shi ne almajiri.
Me kake jira? Me ya sa ba za ka ba shi dama ya shigo cikin rayuwarka ba? Yesu Kiristi ya mutu bisa gicciye na kalbari musamman domin ka samu ’yanci, haka ya karya ikon zunubi domin ka samu kubuta; wane dalili kake da shi na ci gaba da zama cikin zunubi? Watakila kana tunani; kana gaya wa kanka, cewa mai yiwuwa za ka iya lallabawa! Yesu Kiristi ya yi magana cikin Littafin Ruya ta Yohanna 3: 20, “Duba ina tsayawa a bakin kofa ina kwankwasawa, Idan kowane mutum ya ji muryata ya bude kofa, sai in shiga wurinsa, in ci tare da shi, shi kuma tare da ni.” Duk wanda ya ji wannan murya ya kuma yarda ya bude zuciyarsa domin Yesu Kiristi ya shiga, shi ne zai zama mafarin zama almajiri, idan har ka gayyaci Yesu Kiristi cikin rayuwarka, to, ka gayyaci ainihin rai ke nan, ainihin Rai na Yesu Kiristi da kansa, haka kuma za ka gayyaci tabi’arsa zuwa cikinka. Wannan shi ne zai zama mafarin sabuwar rayuwa, a wannan lokaci ne kuma za ka iya bada kanka gare shi daga zuci a cikin almajiranci domin ya horar da kai ya kuma mai she ka abin da yake so ka zama. Wannan shi ne abu na farko da za ka yi cikin zama almajirin Ubangijinmu Yesu Almasihu. Bari Ubangiji Allah Ya taimake ka cikin tunani har ka iya daukar muhimmin wannan mataki na gayyatar Yesu Kiristi cikin rayuwarka idan ba ka rigaya ka yi ba.
Almajiri mutum ne wanda bisa ga yardar ransa ya yanke shawarar daukar karkiyar Yesu Kiristi a wuyarsa. A cikin Littafin Matta 11:28 – 30 Yesu da kansa ya yi magana ya ce: “Ku zo gare ni dukanku da kuke wahala, masu nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku dauka wa kanku karkiyata, ko koya daga wurina: gama ni mai tawali’u ne, mai kaskantar zuciya, za ku samu hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai sauki ce, kayana kuma marar nauyi.”
Wannan ya zama dalilin rayuwar kowane mai bi; idan har za ka zama cikakken almajiri dole dalilin zuwan Yesu Kiristi cikin duniya ya zama dalilin rayuwarka ta yau da kullum. Ko kai malami ne, ko kuwa likita, ko alkali ne, ko kuwa kai mai wa’azi ne, ka bari dalilinka na rayuwa ya zama dalilin zuwan Yesu Kiristi cikin wannan duniya. Idan muka sake duba inda muka yi karatu a cikin aya ta 28, za mu lura da kalmar hutawa wadda Yesu Kiristi ya yi magana a kai, daban da wadda ya yi magana cikin aya 29 wadda ya zama dole kowane mai bi ya nema; mene ne manufar wannan? Yesu Kiristi ya yi alkawarin ba da hutawa ga kowane mutum da ke wahala, mai fama kuma ko a karkashin zunubi, ko rashin lafiya, ko kuwa watakila ma karkashin ikon aljani, mulukoki da ikoki, idan har ka zo gare shi; to, ya yi alkawari ya ce, “Ni zan ba ku hutawa.” Da zarar mutum ya shigo inuwar Ubangiji Yesu Almasihu, gaskiya za a ba shi hutawa daga zunubi, Shaidan da kuma duniya. Amma sai mu tuna cewa ba ita ba ce karshen nassin ba. Sau da dama; mutane da yawa suna tsammani cewa; domin ta wurin alherin Allah sun samu warkaswa cikin jikunansu, kuma sun karbi gafarar zunubansu, wannan ita ce karshen nufin Allah a tunaninsu; amma a gaskiya akwai wani hutu da Yesu ya yi magana a kai, wannan shi ne na aya ta 29 wadda take cewa ku dauka wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai tawali’u ne, mai kaskantar zuciya, za ku samu hutawa ga rayukanku. Wannan shi ne almajiranci. Za mu kara duba wannan sosai idan Maiduka Ya bar mu cikin masu rai, mako mai zuwa.
Zaben kasa na gabatowa, mu ci gaba da rokon Allah Ya ba mu salama da zaman lafiya lokacin zaben da kuma bayan zaben da za a yi. Ubangiji Ya taimake mu, amin.