Almajiri ya kona amarya kan ba shi abinci kadan
Wani almajiri ya kona fuskar wata amarya da abinci mai zafi saboda ta ba shi abinci kadan lokacin da ya je bara gidanta.Amaryar mai suna Zainab danjuma da ke zaune a Unguwar Hotoro a birnin Kano ta kai karar almajirin a ofishin ’yan sanda na unguwar,wadanda su kuma suka mika batun zuwa kotu.Zainab danjuma wacce […]
Wani almajiri ya kona fuskar wata amarya da abinci mai zafi saboda ta ba shi abinci kadan lokacin da ya je bara gidanta.
Amaryar mai suna Zainab danjuma da ke zaune a Unguwar Hotoro a birnin Kano ta kai karar almajirin a ofishin ’yan sanda na unguwar,wadanda su kuma suka mika batun zuwa kotu.
Zainab danjuma wacce ta bayyana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke da Lamba 7 a Unguwar Fagge da kumburarriyar fuska mai miki ta shaida wa kotun cewa a ranar da lamarin ya faru almajirin ya zo gidanta bara, a cewarta saboda ganin halin da yake ciki sai ta karbi kwanonsa ta zuba masa shinkafar da take dafawa a lokacin, sai dai bayan ya karbi abincin ne sai ya juye mata a fuska tare da shaida mata cewa abincin da ta ba shi ya yi kadan ba kuma zai kosar da shi ba.
Yayin da ake karanta masa laifinsa, wanda ake zargin mai suna Abdulmumini Ahmed bai musanta laifin da ake zarginsa ba, laifin da ya saba wa sashi na 159 na Kundin Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta shekarar 2000.
Mai shari’a Abdu Abdullahi Waiya ya dage saurarar shari’ar zuwa ranar 16 ga Oktoba don yanke hukunci tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin.