Almajirin da aka kona wa hannuwa ya nemi a bi masa hakkinsa

Bayan da ya rasa yatsu sakamakon konewar da hannuwansa suka yi, rayuwa ta canja wa almajiri Musa Ahmad kasancewar ba ya iya gudanar da ayyukan da ya saba da su. Idan za a iya tunawa a watan Oktoba da ya wuce ne Aminiya ta kawo rahoton yadda wani gardi ya kone hannuwan almajiri mai suna […]

Almajirin da aka kona wa hannuwa ya nemi a bi masa hakkinsa

Bayan da ya rasa yatsu sakamakon konewar da hannuwansa suka yi, rayuwa ta canja wa almajiri Musa Ahmad kasancewar ba ya iya gudanar da ayyukan da ya saba da su.

Idan za a iya tunawa a watan Oktoba da ya wuce ne Aminiya ta kawo rahoton yadda wani gardi ya kone hannuwan almajiri mai suna Musa Ahmad dan asalin garin Jahun a Jihar Jigawa a makarantar allonsu da ke Unguwar Sabuwar Gandu cikin birnin Kano.
Lamarin ya faru ne a lokacin da Musa mai kimanin shekara 13 ya gaza aiwatar da wankin da gardin mai suna Hambali ya sanya shi, inda Hambalin ya tafasa ruwa ya tsoma hannun Musa a ciki.
Aminiya ta rawaito cewa bayan lamarin ya faru ba a kai yaron asibiti ba, sai aka kai shi ajiya wata makarantar aka damka shi ajiya a hannun wani Alaramma, lamarin da ya jawo hannun ya rube.
Binciken Aminiya ya gano cewa wadansu mutane ne a Unguwar Sabuwar Gandu da suka ga yanayin hannun Musa suka dauke shi zuwa asibiti, inda ma’aikatan asibiti suka sanar da ’yan sanda.
Likitoci a Asibitin Malam Aminu Kano sun yi aiki a hannun Musa ta hanyar yanke wasu yatsun da suka rube.
Aminiya ta gano cewa kimanin kwanaki uku da likitoci suka sallami Musa, iyayensa sun gaza biyan kudin asibitin da ake bin su na Naira dubu 90.
Malma Sa’adatu, markiyar Musa wacce ke jinyarsa a Asibitin Malam Aminu Kano ta shaida wa Aminiya cewa suna cikin halin ni-’ya-su a asibitin inda ta ce: “A yanzu haka duk abin da ke hanunmu ya kare wallahi abinci ma bayin Allah da muke daki daya suke ba mu, ga shi an sallame mu ko kudin motar komawa garinmu ba mu da shi ballantana mu iya biyan bashin da asibitin ke binmu, don haka muna rokon gwamnati da sauran jama’a su taimaka mana.”
Mahaifin Musa Malam Ahmadu Dawaki ya shaida wa Aminiya cewa a bangarensa ya yafe wannan abu da aka yi wa dansa saboda malamin yaron dan uwansa ne. “Tun daga lokacin da lamarin ya faru na ce na yafe, domin ba zan yi shari’a da malamin da yake dan uwana ne ba,” inji shi.
Sai dai Malam Ahmadu ya nemi gwamnati da sauran jama’a su kawo musu dauki domin su biya bashin asibiti na Naira dubu 90. Ya ce likitoci sun ce za a rika kai yaron gashi, kuma za a sake yi masa wani aikin bayan kwana biyu, don haka suna neman a taimaka musu.
Sai dai a tattaunawar da Aminiya ta yi da almajiri Musa wanda ya yi magana takaici saboda yunwar da take damunsa ya ce shi bai yafe zaluncin da aka yi masa ba. “Ni dai ban yafe ba ina neman hukuma ta rama min,” inji shi.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya game da halin da wadanda ake zargin suke ciki, ya ce iyayen Musa sun kai shi karatu ne wani gari da ake kira Nassarawan-Doya kusa da garin Makarfi a Jihar Kanduna a hannun wani malami mai suna Malam Is’hak Usaini kafin wannan waki’a ta same shi a lokacin da malamin ya yi tafiya ya damka almajiransa a hannun babban almajirinsa Hambali. “Bayan Musa ya samu rauni maimakon su kai shi asibiti sai suka dauko shi daga can suka kawo shi wurin wani malami dan uwansu da ke Unguwar Sabuwar Gandu don a yi jinyarsa, kuma a ranar 24 ga Oktoba ne mutanen unguwar suka sanar da ’yan sanda halin da ake ciki. Kuma nan take muka kama wadanda ake zargin muka gabatar da su a gaban Kotun Majistare ta Gyadi -Gyadi a ranar 21 ga Nuwamba,” inji shi.
Ya ce dukkan wadanda ake zargin sun musanta kona Musa, inda suka ce yaron ne ya dame su da fitina sai suka sanya shi a wani daki suka kulle, kuma a kokarinsa na guduwa ne ya sa hannunsa a tagar dakin ya samu raunuka. Ya ce alkalin kotun ya ba da umarnin a tsare su a kurkuku zuwa ranar 21 ga wannan wata don ci gaba da sauraron shari’ar.