Almundahana: A Ingila ya kamata a hukunta Diezani ko a Najeriya?
Tsohuwar Ministan Fetur a zamanin Shugaban kasa Goodluck Jonathan, Misis Diezani Allison Maduewke na fuskantar zarge-zargen almundahanar kudi daban-daban, inda a yanzu haka take Ingila. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya kamata a hukunta ta a can Ingila ko kuwa a dawo da ita Najeriya ta fuskanci hukunci a gida? Ga ra’ayoyin […]
Tsohuwar Ministan Fetur a zamanin Shugaban kasa Goodluck Jonathan, Misis Diezani Allison Maduewke na fuskantar zarge-zargen almundahanar kudi daban-daban, inda a yanzu haka take Ingila. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya kamata a hukunta ta a can Ingila ko kuwa a dawo da ita Najeriya ta fuskanci hukunci a gida? Ga ra’ayoyin mutane daban-daban kan al’amarin:
Hukunci a gida ya fi – Jamilu Shu’aibu
Ahmed Kabir S/kuka, a Katsina
Jamilu Shu’aibu: “Farko sai mu fara kallon laifuffukan da ta aikata. A kasar waje dai kudin ne suka gani ta kai masu da nufin boyewa. A wajensu ta mallaki dukiyar ba bisa ka’ida ba amma a nan gida ai nan ne ta kwashi kudin ko in ce ta saci kudin ta kai waje saboda haka nan ta yi wa barna, nan kuma ya dace a hukunta ta, domin hakan zai zama darasi ga wasu. Kuma hakan zai kara tabbatar wa duniya cewa mu ke da ’yancin kanmu kuma muna da doka da kuma masu shari’a ba, sai mun je waje ba. Kuma ita wannan gwamnati lallai ta nuna da gaske take yi wajen yaki da almubazzaranci da dukiyar kasa. Saboda haka, Diezani hukuncin gida ya fi dacewa da ita ba na waje ba.”
A dawo da ita Najeriya – Najja’atu Musa
Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna
Najja’atu Musa Musa: “A ra’ayina, ya kamata a dawo da tsohuwar Ministar albarkatun man fetur Diezani Allison Maduekwe Najeriya don a yi mata shari’a a kotun gida. Dalilin fadin haka kuwa shi ne, ai ta aikata laifin ne a Najeriya kafin ta tsere Ingila. To in son samu ne ya kamata ne a hukunta ta a gaban ’yan kasa don ya zama darasi ga masu neman aikata irin haka. Kodayake idan an yi mata hukunci a kotun Ingila babu laifi amma idan an dawo da ita gida Najeriya abin zai fi yin armashi kuma ’yan kasa za su fi gamsuwa da cewa lallai gwamnati da gaske take wajen hukunta ta a kan irin almundahanar da ta tafka a kasar nan. A takaice dai na goyi bayan a dawo da ita Najeriya don ta fuskanci shari’a a kotun da ke kasar nan.”
A hukunta ta a Najeriya – Kabiru Lahira
Nasiru Bello, a Sakkwato
Kabiru Lahira Dandinmahe: “A Najeriya ya kamata a hukunta ta don a nan ne ta aikata laifin ba a kasar Ingila ba. Yi mata hukuncin a nan shi ne adalci, duk wata tuhuma da ake yi mata a Najeriya ne ta aikata laifin, duk wata hujja da ake nema nan ne take, duk wasu shaidu ma a nan suke da zama, hukuncin da za a yanke mata bayan shari’a, mutanenta ake son su san an yi mata adalci ko akasin haka, kuma mutanen kasar nan na da hakkin sanya ido ga shari’ar don su ne aka yi wa zamba cikin aminci.”
A hukunta ta a Najeriya – Kabir Ibrahim
Ahmed Kabir S/kuka, a Katsina
Kabir Ibrahim Sha’iskawa: “Batun a kai Diezani kasar waje don yi mata hukunci bai ma taso ba. A hukunta ta a gida shi ne, domin zai zamo ishara ga saura da kuma nuna karfin wannan gwamnati da ke ci a yanzu. Ganin irin hukuncin da za a yi mata zai hana wani ko wasu koda sun yi niyyar aikata irin wannan laifin su fasa. Sannan kuma wannan hukuncin zai kara nuna cewa satar kudin jama’a ba zai sa mutun ya yi arziki ba kuma zai fuskanci hukunci ko dai a nan duniya ko a lahira.”
A dawo da ita gida – Hannatu Abdullahi
Nasiru Bello, a Sakkwato
Hannatu Abdullahi Baba: “A hukunta ta a nan zai fi dacewa da zargin da ake yi mata. maido da ita gidai a yi mata hukunci zai kara tabbatar da adalcin gwamnati. Kudin kasar nan ta kwasa, duk inda ta kai su ba na can ba ne kuma Najeriya na da dokokin kasa, ita ’yar kasar ce; da dokar kasarta ne ya fi dacewa a hukunta ta, ba da wata dokar Ingila ba. Kawai dai mu za mu yi wa Ingila godiya da ita ce ta fara bankado lamarin amma ba mu yarda a hukunta ’yar kasarmu a wajen kasa ba, don mun fi son a yi mata adalci a nan, don na baya su gani su tsorata da lamarin, su kiyaye kansu; sabanin in an yi hukunci can wani wuri, wa ya gani har ya san abin da ya faru balle ya kiyaye?”
A tuhume ta a nan gida – Ummu Adiyya
Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna
Ummu Adiyya Mahmud Mustapha: “Gaskiyar Magana ita ce, idan muka yi la’akari da cewa mace ce ta tafka irin wannan mummunar ta’asa wajen satar dukiyar al’ummar kasar nan, za mu iya cewa tabbas ta ba mata kunya. Ana daukar mata a matsayin wadanda suka fi dama-dama wajen kwatanta gaskiya da rikon amana a duk lokacin da aka ba su wani mukami amma yadda tsohuwar Ministar kula da albarkatun Man fetur a zamanin mulkin Goodluck Jonathan, Diezani Allison Madueke ta tafka sata abin ya wuce hankali. A kullum sai ka ji yadda Hukumar EFCC ta kwato dukiyoyin da wannan mata ta sace, abin takaici ne. A ra’ayina, zai fi kyau ne a dawo da ita gida don a hukunta ta a daya daga cikin kotunan da ke kasar nan don ya zama darasi a gare ta da kuma na baya masu son aikata irin haka. Da ma ta gudu zuwa Ingila ne don kada ta fuskanci hukunci, to idan an dawo da ita gida hakan zai nuna lallai laifin da ta aikata yana da girma kuma ’yan kasa za su gamsu da cewa lallai za a iya hukunta kowane mutum komai matsayinsa.”