Almundahana: Betta Edu ta kai kanta ofishin EFCC

Betta Edu, ta kai kanta Hedikwatar Hukumar EFCC domin amsa tambaoi kan badakalar kudin tallafi.

Almundahana: Betta Edu ta kai kanta ofishin EFCC

Dakatacciyar Ministar Jinkai, Betta Edu, ta kai kanta Hedikwatar Hukumar yaki da Masu Karya Tattalin arziki (EFCC) domin amsa tambaoi kan badakalar kudin tallafi.

Betta Edu za ta amsa tamboyoyi ne washegarin da Shugaba Tinubu ya dakatar da ita, ya kuma umarci Ministan Kudi, Wale Edun ya jagoranci kwamitin bincikar ta, gami da kuma toshe duk wata kafar da ake almundahana a harkar kudin tallafin gwamnati a ma’aikatar.

A ranar Litinin da Tinubu ya dakatar da ita aka hana ta yin ido hudu da Shugaba Tinubu, aka soke izininta na shiga Fadar Shugaban Kasa.

Kasa da minti 30 da dakatar da Betta Edu ne EFCC ta sanar da gayyataeta kan badakalar karkatar da kudaden tallafin masara karfi na jihohi hudu.

A ’yan makonnin nan dai zargin almundahana ya dabaibaye ma’aikatar jinkai, inda ake bincike kan harkokinta na shekaru shida da suka gabata.

A baya-banan nan aka bankado bakaladar karkatar da kudaden tallafin masu karamin karfi kimanin Naira biliyan 44 daga Ofishin Kula da Rabon Tallafin Dogaro da Kai.

Ana zargin shugabar hukumar, Halima Shehu, ta tura kudaden zuwa asusun ajiyar wasu mutane da kamfanoni ba bisa ka’ida ba.

Daga bisani kuma wata sabuwa ta kunno kai bayan Betta Edu ta aike wa Ofishin Akanta-Janar na Kasa takardar neman ofishin ya tura Naira miliyan 585 zuwa asusun wata mata.

Betta ta ce matar akanta ce a ofishin kula da tallafi a wasu jihohin kudu hudu, amma duk da aka ofishin Akanta-Janar ya ki, da cewa yin hakan ba aikinsa ba ne.

Akwai kuma zargin facaka da kudaden ma’aikatar bayan bullar wata dakarda dauke da sa hannun Betta Edu na biyan kudin tafiyar aikin jami’an ma’aikatar zuwa wani fili jirgin sama da babu shi a Jihar Kogi.

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania

An ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda