Almundahana: Ko ya dace Buhari ya faro bincike daga 1999?

Gwamnatin Jonathan kadai ya kamata – Musa Hamidu A.A. Masagala, a Benin Musa Hamidu: “Ni a ra’ayina da kuma irin fahimtar da na yi wa wannan bayanin shi ne, ba laifi ba ne a yi wannan binciken sai dai a ra’ayina idan Shugaba Buhari zai yarda da tawa shawarar, ya kamata kada bincikensa ya wuce […]

Almundahana: Ko ya dace Buhari ya faro bincike daga 1999?
Almundahana: Ko ya dace Buhari ya faro bincike daga 1999?

Gwamnatin Jonathan kadai ya
kamata – Musa Hamidu

A.A. Masagala, a Benin

Musa Hamidu: “Ni a ra’ayina da kuma irin fahimtar da na yi wa wannan bayanin shi ne, ba laifi ba ne a yi wannan binciken sai dai a ra’ayina idan Shugaba Buhari zai yarda da tawa shawarar, ya kamata kada bincikensa ya wuce kan gwamnatin da ya gada a 2015. Dalilina kuma shi ne, domin tsofaffin rubabbun kayan gaba daya za a same su a cikin gwamnatin nan da ta shude a 2015, saboda haka ba sai an soma daga 1999 ba. Yin hakan zai iya kawo wa wannan sabuwar gwamnatin tsaiko a wani sashi na muhimman ayyukanta da ta sanya a gaba na ci gaba da walwalar al’ummarta, domin zai zamo babu wani biyan bukata da za a samu na a-zo-a-gani muddin aka ce sai an faro ta daga 1999.”

A bincike su gaba daya – Ibrahim Ahmadu

A.A. Masagala, a Benin

Ibrahim Ahmadu: “Ni a ganina, ai ba sai an nemi wani bayani ba daga wurin jama’a dangane da wannan lamari, tunda kowa ya sani ba zai zama adalci ba idan za a bari masu barna su ci gaba da walwala ba tare da an bincike su ba. Don haka ya zama wajibi a bi su daya bayan daya a bincike su. Dalili kuwa shi ne, su ne suka talautar da kasar nan da karfin tsiya. Don haka bai kamata a yi musu sassauci ba, tun daga gwamnatin da ta shude ta 1999 zuwa ta 2015. Saboda ni ina ganin bai dace ba a ce wasu ’yan tsiraru daga cikin mutane suna kwasar dukiyar kasa ta haramtacciyar hanya suna boyewa a kasashen ketare suna jefa al’ummar kasa a cikin mawuyacin halin rayuwa, sannan a ce an bar su suna holewa. Don haka ya zama wajibi a bincike su kuma a tilasta su sa maido da abin da suka sata daga dukiyar kasa. Da wannan za a samu wa al’umma aiki da dukiyar.”

Kada binciken ya wuce Gwamnatin Jonathan – Fatima Abubakar

Nasiru Bello, a Sakkwato

Fatima Abubakar: “Ni kam ban goyon bayan bincike ya wuce gwamnatin Jonathan. In aka ce sai ya wuce to ba a san lokacin da za a kare wannan binciken ba, don sai kotu ta yanke hukunci ne za a rika samun ci gaba; to kowa a kasar nan ya san yadda kotunan ke tafiyar hawainiya. Wannan babban aiki ne Shugaba Buhari ke son daukowa. Mu talakawa ba mu maraba da shi, don gaskiya a yanzu ma muna ji a jikinmu fiye da gwamnatin baya. Duk da mun san gyara ake yi amma bincike ne ya sanya muke cikin halin matsin rayuwa, to balle a ce a fadada abin zai kara hargitsewa ne kawai, don gidaje da dama suna cikin yunwa, matasa na yin garari komai ya tsaya cik. Ina kira ga Shugaban kasa ya tsayar da bincikensa kan gwamnatin da ya gada kawai ko ya samu lokacin da zai sama mana abubuwan more rayuwa daga kudaden da aka tatsa ga barayin da suka gabata.”

Fadada binciken ya yi daidai – Khalid Silame

Nasiru Bello, a Sakkwato

Khalid Silame: “Ina goyon bayan Shugaban kasa kan ya fadada binciken tun daga 1999 saboda a yi daidaito. In ka duba za ka ga kamar kusan manyan al’ummar da muke da su a kasar nan, Yarabawa da Hausawa da Ibo sun jagoranci kasar a wannan siyasar da muke ciki. In aka binciki gwamnatin da ta gabata, aka bar wata, wasu sai su ga ba a yi musu adalci ba; an dauki wasu ne shafaffu da mai. Magana ta gaskiya hadin kan kasar nan yana cikin binciken Gwamnatin Obasanjo zuwa wadda Shugaba Buhari ya gada. Kan haka nake cewa fadada bincike ya yi daidai, don duk badakalar da aka yi daga can ta fara.”

A fara daga lokacin Jonathan – Shafi’u Idris

Rabilu Abubakar, a Gombe

Shafi’u Idris: “Ni a ganina, kamata ya yi kada Shugaban kasa Buhari ya yi dogon waiwaye, ya fara binciken daga gwamnatin PDP ta Goodluck Jonathan saboda a wannan lokacin ne aka fi samun mummunar sata. Idan aka ce za a fara bincike tun daga lokacin gwamnatin Obasanjo, binciken zai yi tsawo kuma zai dauki lokacin da zai hana a fara gudanar wa ’yan Najeriya ayyukan ci gaba. Don haka ne nake ba da shawarar a fara daga shekarar 2007. Duk wanda aka kama, a yi masa hukunci daidai da laifin satar da ya yi.”

Ya dace a faro daga 1999 – Maryam Hassan

Rabilu Abubakar, a Gombe

Maryam Hassan Muhammad: “Idan dai kudaden da aka sace din za su dawo, ya dace a binciki duk wani wanda ya yi sata saboda sun jefa kasar cikin wani hali na fatara da talauci. Ga rashin hanyoyi da kayayyakin more rayuwa musamman ga talaka. Abin da ya sa na ce haka shi ne saboda mutanen da suka wawure kudin ba su da kishi, domin sun kwashe kudinmu sun kai kasashen waje, ba su amfanar kowa.
“Shugaban kasa Buhari ya binciki kowa tun daga 1999 har zuwa yanzu, ba sai daga shekarar 2007 ba saboda a wadancan shekarun aka fara sace kudin talakawan Najeriya.”