Almundahana: Kotu ta aike da tsohuwar Minista gidan gyaran hali

Kotun dai ta daure su wata uku a gidan gyaran hali.

Almundahana: Kotu ta aike da tsohuwar Minista gidan gyaran hali

Kotu

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jos, babban birnin Jihar Filato ta aike da tsohuwar Ministar Ruwa, Sarah Ochekpe, zuwa gidan gyaran hali.

Kotun ta kuma aike da karin wasu karin mutum biyu; Raymond Dabo da Evangelist Leo Sunday Jitung hukuncin daurin wata uku kowannensu.

Mutane ukun dai na fuskantar tuhume-tuhume ne tsawon shekara hudu kan zargin hada baki don yin almundahanar wasu kudade.

Sai dai kotun ta bayar da zabin biyan tarar Naira miliyan daya ga kowannensu.