Almundahana: Kotu ta kwace gidajen mai 10 a hannun wani soja
Babban sojan da aka kwace kadarorin a hannunsa hadimi ne ga Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaron Kasa, Babagana Monguno.
Wata babbar kotun tarayyar Najeriya ta kwace gidajen mai guda 10 da wasu kadarori 14 daga hannun wani babban soja da ta kama da laifin satar kudaden gwamanti.
Gidajen man na daga cikin kadarori 24, da suka hada da taskar iskar gas da gine-ginen shaguna da wurin taro da kamfanoni, wadanda kudinsu ya kai Naira biliyan 10.9 wadanda kotun ta kuma mallaka wa Gwamnatin Tarayya.
- Yadda ’yan Najeriya ke kokawa bayan litar fetur ta kai N600
- An tona asirin manyan ’yan sanda da jami’an NDLEA bayan Abba Kyari ya kwana a tsare
Daga cikin kadarorin da aka kwace akwai gidajen mai tara, ciki har da mai kan famfo 41 da mai kan famfo 39.
Akwai kuma tashar iskar gas daya da gine-ginen shaguna masu hawa uku guda biyu masu shaguna 154, da kamfanin robobi, da wurin taro da kuma manyan filaye, duk a Kano.
Akwai kuma kamfanin robobi da kamfanin bulo da shaguna da wurin taro da sauransu a jihohin Kaduna da Borno da Kuros Riba.
Kotun da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin kwace kadarorin ne baya Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar da karar zargin babban sojan da wawure kudaden gwamnati.
Alkalin kotun, Mai Shari’a N.E. Maha ne ya bayar da umarnin a zaman kotuna na ranar Talata.
Babban sojan da aka kwace kadarorin a hannunsa hadimi ne ga Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaron Kasa, Babagana Monguno.