Zargin N33bn: Tsohon ministan lantarkin Buhari ya sume a kotu

Tsohon ministan ya shiga akwatin ba da shaida, inda aka ga wani bangare na tufafinsa a jike sharkaf

Zargin N33bn: Tsohon ministan lantarkin Buhari ya sume a kotu

Tsohon Ministan Lantarki, Injiniya Saleh Mamman

Tsohon Ministan Wutar Lantarki a mulkin tshon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Injiniya Saleh Mamman, ya fadi a kotun da ke sauraron shari’ar zargin sa da badakalar kudade.

Saleh Mamman ya yanke jika ya fadai ne a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, sakamakon rashin lafiya a kodan da ake gurfanar da shi kan zargin karkaar da Naira bilian 33.

Saleh Mamman, wanda aka kai kotun a safiyar Alhamis, ya fadi ne kafin a kira shari’ar, a cewar Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

NAN ya rawaito cewa lauyan tsohon ministan, Femi Ate, SAN, ne ya shaida wa Mai Shari’a James Omotosho hakan jim kadan da aka kira shari’ar.

Da aka ci gaba da sauraren karar, tsohon ministan ya shiga akwatin ba da shaida, inda aka ga wani bangare na tufafinsaa jike sharkaf.

Hukumar EFCC ta shigar da karar Mamman tuhume-tuhume 12 na karkatar da kudade da safarar kudaden haram Naira biliyan 33.

A ranar 10 ga Mayu, 2021, aka kama tare da tsare tsohon ministan da ya yi aiki a karkashin tsohon shugaban kasa Buhari daga 2019 zuwa 2021, a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

A ranar 1 ga Satumba, 2021 ne Buhari ya sallami Saleh Mamman tare da Ministan Noma da Raya Karkara na lokacin, Sabo Nanono a wani abin da ake kira sake fasalin majalisar ministoci.

An zargi Mamman da hada baki da ma’aikatan ma’aikatarsa da ke kula da asusu na ayyukan wutar lantarki na Zungeru da Mambilla don karkatar da kusan Naira biliyan 22.

Binciken ya gano wasu kadarori a Najeriya da kasashen ketare da ake zargin suna da alaka da wadanda ake zargin, yayin da aka ce an kwato miliyoyin Naira da daloli a hannunsa.