Almundahanar N21.5bn: Kotu ta kori karar da aka shigar da tsohon hafsan sojin sama

EFCC ba ta da hurumin binciken wani jami’in rundunar sojin Najeriya har sai ya yi ritaya.

Almundahanar N21.5bn: Kotu ta kori karar da aka shigar da tsohon hafsan sojin sama

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas ta kori karar da aka shigar da tsohon Babban Hafsan Rundunar Sojin Saman Najeriya, Adesola Amosun kan zargin almundahanar N21.5bn.

Kotun ta yi watsi da zargin halasta kuɗin haram da Hukumar Yaƙi da rashawa EFCC ta shigar kan tsohon hafsan sojin saman da wasu mutum biyu.

Ana iya tuna cewa, tun a ranar 26 ga watan Yunin 2016 ne EFCC ta gurfanar da Amosun tare da tsohon Akantan rundunar sojin saman ta NAF, Air Vice Marshal Jacob Bola Adigun da tsohon daraktan kuɗi da kasafi na rundunar, Air Commodore Gbadebo Owodunmi Olugbenga.

Bayanai sun ce EFCC ta gurfanar da su ne a gaban kotun kan tuhume-tuhume 26 da suka shafi wawure kuɗin baitul malin rundunar sojin saman.

Lauyan waɗanda ake tuhuma ya yi kafa hujjar cewa kotun soji ce kaɗai ke da hurumin sauraron karar saboda a lokacin suna bakin aiki.

Kan haka ne kuwa alkalin ya amince da hujjar lauyan da cewa kotun ba ta da hurumin sauraron wannan ƙara saboda a lokacin waɗanda ake zargi suna aiki a matsayinsu na sojoji.

A yayin da yake yanke hukuncin kan ƙarar mai lamba FHC/L/280C/16, mai shari’a Chukwujekwu Aneke ya ce EFCC ba ta da hurumin binciken wani jami’in rundunar sojin Najeriya har sai ya yi ritaya.