Zargin N110.4bn: Kotu ta bada belin Yahaya Bello kan N500m

Dole ne waɗanda za su tsaya masa su kasance fitattun ’yan Najeriya da ke da kadarori a ɗaya daga cikin unguwannin Maitama da Jabi da Utako da  Apo da Guzape da Garki da Asokoro.

Zargin N110.4bn: Kotu ta bada belin Yahaya Bello kan N500m

Wata babbar kotu a Abuja ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello a kan kuɗi Naira miliyan 500 bisa zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati.

Mai shari’a Maryanne Aninih ce ta bada umarnin a ranar Alhamis ta kuma umurci Bello da ya gabatar da waɗanda za su tsaya masa guda uku a daidai wannan adadin kuɗin.

Alƙalin ta ce dole ne waɗanda za su tsaya masa su kasance fitattun ’yan Najeriya da ke da kadarori a ɗaya daga cikin unguwannin Maitama da Jabi da Utako da  Apo da Guzape da Garki da Asokoro.

Alkalin ta kuma buƙaci Yahaya Bello da ya ajiye fasfo ɗinsa da sauran takardun tafiye-tafiye a wurin magatakardar kotun

Ta kuma bayar da umarnin cewa dole ne ya ci gaba da zama a gidan yarin Kuje har sai an cika sharuɗɗan belin.

Mai shari’a Maryann Anenih, a ranar 10 ga watan Disamba, ta ƙi amincewa da buƙatar belin tsohon gwamnan, tana mai cewa an shigar buƙatar ne da wuri.

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele