Al’Mustapha ya maka Sheikh Sanusi Khalil a kotu
Tsohon dogarin marigayi Sani Abacha, Manjo Hamza Al’Mustapha ya shigar da kara a babban kotun Shari’a da ke titin Daura a garin Kaduna, inda yake tuhumar wani malamin addinin Musulunci, Shaikh Sanusi Khalil da bata masa suna da kuma cin mutunci, da ya yi a cikin hudubarsa.Ya ce Sheikh Sanusi Khalil ya ci mutuncin nasa […]

Tsohon dogarin marigayi Sani Abacha, Manjo Hamza Al’Mustapha ya shigar da kara a babban kotun Shari’a da ke titin Daura a garin Kaduna, inda yake tuhumar wani malamin addinin Musulunci, Shaikh Sanusi Khalil da bata masa suna da kuma cin mutunci, da ya yi a cikin hudubarsa.
Ya ce Sheikh Sanusi Khalil ya ci mutuncin nasa ne a ranar wata Juma’a ta watan Disamba na shekarar 2013 a masallacin Juma’a na Sani Zangon Daura a Kaduna.
A takardar shigar da karar da lauyan wanda ke kara Sadau Garba ya sanya wa hannu a ranar 22 ga watan Afiriu, an bayyana cewa batancin da malamin ya yi an buga su ne a ciki faya-fayan CD da DbD kuma an dauka ne da sanin wanda ake kara.
Shi dai Shaikh Sanusi Khalil an ce ya yi wadannan kalamai ne na batanci a kan Manjo Almustapha a cikin hudubarsa, inda yake zargin Almustaphan da koya wa wadansu yara yadda za su kashe mutane, kamar yadda tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi zargi a wasikar da ya aika wa Shugaba Jonathan a watannin baya.
Aminiya, wacce ta ziyarci kotun, ta ruwaito cewa an jibge ’yan Sanda da Sojoji a kotun rike da makamai cikin shirin ko-ta-kwana. Kuma ba kowa suke bari ya wuce zuwa cikin kotun ba domin gudun kada wadansu su kai hari a wajen.
Sai dai bayan sa’o’i da halartar wanda ke kara da sauran mutane, sai aka ce Alkali Mustapha Umar bai samu zama domin sauraron karar ba, don haka sai aka dage sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Mayun wannan shekarar ta 2014.
Manjo Al’Mustapha ya bayyana wa manema labarai, a wajen kotun cewa, ya je kotun ne domin kare martabar Musulunci da Arewa da kuma wanke kansa daga kazafin da ya ce an yi masa. “Babu abin da ya yi mini zafi, abu ne ya faru da muke kuma kallonsa a musulunce da kishin kasa da kuma kishin Musulunci da kuma kare martabar Musulunci da musulmai da zaman lafiyar Arewa da Najeriya baki daya.
Ya ci gaba da cewa, ya kai kara kotun Musulunci ne domin a bayyana gaskiya a kuma yi shari’a da Alkur’ani da hadisan Manzon Allah (SAW). “Malam ya yi maganganu a faifan bidiyo kuma ba na jin a kasar nan akwai wanda aka yi wa kazafi a ’yan watannin nan kamar yadda aka yi min. Wannan kazafin yana nan, kuma burina shi ne a zo a tattauna abin da duk ya fada, inda za a dauki Alkur’ani a rantse da shi a bainar jama’a.
“Domin akwai abubuwa da dama da zan fada, wanda hadari ne ga Najeriya kuma hadari ne ga Musulunci da musulmai, wanda ya kamata a gyara. Wasa da Alkur’ani, wasa da shari’a, wasa da Musulunci, son kudi ko munafunci, ba abin yarda ba ne. Hakki ne a kanmu mu tsaya mu bi gaskiya tsakani da Allah. Idan karar da na yi ta saba wa dokar Musulunci a shirye nake in dauki duk abin da za a yi mini. Na zo kotu ne saboda kare mutuncin Musulunci da Arewa,” inji shi.
Shi kuwa Malam Sanusi Khalil, a takaitaccen jawabin da ya yi wa manema labarai , cewa ya yi ba zai ce wani abu ba sai abin da kotu ta ce, tun da dai an rigaya an shigar da kara a gabanta.