Almustapha ya ziyarci ’yan Arewa a Legas
Babban dogarin tsohon Shugaban kasa, marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Almustapha mai ritaya, ya kai ziyarar bangajiya ga ’yan Arewa mazauna Legas, wadanda suka yi ta fadi-tashi a lokacin da yake a daure a kurkukun Kirikiri a Legas.Ya bayyana cewa ya yi ziyarar ban girma da godiya ne ga ’yan Arewa mazauna Legas, bisa […]
Babban dogarin tsohon Shugaban kasa, marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Almustapha mai ritaya, ya kai ziyarar bangajiya ga ’yan Arewa mazauna Legas, wadanda suka yi ta fadi-tashi a lokacin da yake a daure a kurkukun Kirikiri a Legas.
Ya bayyana cewa ya yi ziyarar ban girma da godiya ne ga ’yan Arewa mazauna Legas, bisa irin kauna da goyon baya da suka nuna masa. Ya kuma nemi hadin kansu domin yin aiki tare don ci gabansu a harkokin kasuwancinsu da ayyukansu a wannan bangaren.
Ya kuma sha alwashin tallafa wa kungiyoyi da matasa. “Duk tafiye-tafiye da ka ga ina yi, muna kai-kawo ne don samar wa matasa ayyukan yi, muna kulla kyawawan alakoki da kungiyoyin taimakon juna a wannan bangare na kasar nan.” Inji shi.
Shugaban kungiyar matasan dillalan shanu ta kasuwar Abbatuwa a Legas, Alhaji Muhammad Tom ya shaida wa Aminiya cewa ganin yadda suka jajirce, suka yi ta kai gauro da mari a lokacin da Hamza Almustapha yake a daure, inda suka yi da jininsu da lokacinsu da dukiyoyinsu; hakan shi ne ya sanya ya zo ya nuna godiyarsa a gare su, domin abin da suka yi masa ba zai iya saka masu ba.
Ya ce Hamza Almustauntfa ya nuna godiyarsa a gare su, ya fada musu cewa su kara hakuri, domin duk wanda ya sha wuya zai ji dadi kuma ya gabatar musu da mutum biyu wadanda za su tuntuba in suna da wata bukata; domin ya ce a shirye yake ya tallafa wa matasansu da suka kammala karatu da kuma masu sha’awar kwallon kafa a cikinsu.
A nasa bangaren, Alhaji Ado Shu’aibu dansudu, shugaban kungiyar hadin kan ’yan Arewa, nuna rashin jin dadinsa ya yi bisa rikon sakainar kashin da Hamza Almustapha ya yi musu tun bayan da aka sako shi.
“Mun ji ziyarar tasa ce a shanun huda kuma mun yi mamakin haka, abin kuma ya daure mana kai, domin kungiyarmu ta Arewa United; ita ce ta fara gayyato Fedrick Fashehun, shugaban kungiyar Yarabawa ta OPC; muka ce masa ya dubi matsayinsa na dattijo ya zo a yi fafutukar fitar da Hamza Almustapha da shi. Haka za mu yi jerin gwano mu je kotu, duk lokacin da za a yi shari’arsa, muna daga kwalaye. Tun ana jifarmu, ana ce mana ole-ole (barayi), haka muka jure, haka muka yi ta yi fiyi da shekaru goma. Ai ka ga an ci moriyar ganga, an yada kwaurenta.” Inji Ado dansudu.