Al’umar Michika sun koka da Gwamnatin Tarayya da ta Adamawa

Al’umar karamar Hukumar Michika dake Jahar Adamawa sun koka da gwamnatin Jahar Adamawa da ma ta tarayya, wadda a cewarsu an share su tun lokacin da Boko Haram ta kai musu harin da ya rusa gidaje da kuma dukiyoyinsu. Mazauna Michikan dai sun bayyana hakan ne ga wakiliyar Aminiya, a lokacin da suke taron al’adunsu […]

Al’umar Michika sun koka da Gwamnatin Tarayya da ta Adamawa

Al’umar karamar Hukumar Michika dake Jahar Adamawa sun koka da gwamnatin Jahar Adamawa da ma ta tarayya, wadda a cewarsu an share su tun lokacin da Boko Haram ta kai musu harin da ya rusa gidaje da kuma dukiyoyinsu.

Mazauna Michikan dai sun bayyana hakan ne ga wakiliyar Aminiya, a lokacin da suke taron al’adunsu wadda suke gudanar wa duk shekara. Suka ce babu makarantu masu kyau domin an rusa, sannan gadajensu ma an rusa ga rashin wutan lantarki tun lokacin da Boko Haram ta kai musu harin farko ba a gyara komai ba, kuma a halin yanzu duk sun dawo gida.

Wani mazaunin Michika Bitrus Jabu Sohi ya ce su mutane ne masu kwazo da hazaka don haka sun hada kansu sun gyara wadansu gidajen da aka rusa ba tare da tallafi daga gwamnati ba. Ya jinjinawa wani Kwache Iliya wadda ya dawo da al’addunsu na gargajiya wadda ake kira ‘Kamwe’ ya ce gudanar da wannan bikin al’adar na kara hade kawunansu.

Wani mai suna Aled ya ce fiye da shekaru hudu da suka gabata, babu wutar lantarki a garin, kuma karfe takwas ko tara na yi na dare kowa zai shige gida. Ya ci gaba da cewa, ba za su manta da irin kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi musu ba wajen kawo karshen ‘yan ta’adda, sai dai yana da kyau a sake waiwayarsu a cewarsa.

 

Kofin Duniya: Jamus ta lallasa Curaçao da ci 7 a wasan farko

Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai