Al’umma kada a yaudare mu
Al’ummar Najeriya kada mu yarda ’yan siyasa su yaudaremu, musaman ganin yadda zabe ke karatowa, masu mulki za su yi ta yin alkawuran da ba za su iya cikawa ba. Don haka talakawa da ’yan adawa da kungiyoyin kwadago kan lallai mu fitar wa masu mulki jerin bukatunmu, ta yadda ba za su yaudaremu, su […]
Al’ummar Najeriya kada mu yarda ’yan siyasa su yaudaremu, musaman ganin yadda zabe ke karatowa, masu mulki za su yi ta yin alkawuran da ba za su iya cikawa ba. Don haka talakawa da ’yan adawa da kungiyoyin kwadago kan lallai mu fitar wa masu mulki jerin bukatunmu, ta yadda ba za su yaudaremu, su kwashe dukiyar kasa, su bar mu cikin halin ha’ula’i.
Yau jam’iyyar APC, wadda ake ganin ita ce babbar jam’iyyar adawa a kasar nan, ya kamata ta gyara gidanta, kada ta bari jam’iyyar PDP ta wargaza ta, tunda ba za ta daina yi mata kulle-kulle ba, musamman saboda ba ta bukata ’yan Najeriya su samu sauyin rayuwa mai kyau. Kwanan nan bom ya yahalaka mutane a Yanya ta Birnin Tarayya Abuja, amma babu abin da ya fito daga bakin kakakin PDP, sai kawai cewa ya yi, “Jam’iyyar adawa ta APC ce ta dasa shi.”
Wani shirin na wargaza ‘’yan adawa, shi ne, ana zargin APC da kokarin musuluntar da Najeriya, ta hanyar fitar da ‘’yan takara, Shugaban kasa da Mataimakinsa musulmi, wato abin da a Turance suke kira “Musulim-Musulm ticket.” daukacin irin wadannan al’amura, ya kamata al’ummar Najeriya su dauka yaudara ce kawai. Kuma masu furta irin wadannan maganganub, suna yi ne don kawai ka ’yan adawa da kungiyoyin kwadago su yi yunkurin kawar da PDP, ko al’umma ta samu ingantacciyar rayuwa.
Ko mun ki, ko mun so, sai daukacin ’yan Najeriya sun hada kai, wajen yaki da bambance-bambancen addinin da kabilanci. Uwa-uba, mu tsayu kan duk wani abu da zai hada kan al’umma, ta yadda masu mulki ba za su yaudaremu ba. Watakila ma idan muka yi wannan yunkurin, su ma masu muguwar manufa, su samu sauyin ra’ayi.
Don haka nake karkare kirana ga masu kishin jam’iyyar adawa ta APC, wato APC forum da Janar Muhammad Buhari da Bola Ahmad Tinubu da Shugaban Forum Alhaji Abubakar baure da Shugaban kwadago, Omar AbdulWahid, kan lallai su jajirce, wajen ganin kowace irin gwamnati aka kafa bayen zaben 2015, ta himmatu kacokam wajen samar wa al’umma ilimin zaman ingance da tsarin kula da lafiya da kyautata zamantakewa da tsaron rayuka da dukiya. Uwa-uba, a inganta harkokin shari’a a kotunan kasar nan, ta yadda talaka zai rika samun adalci a duk sa’adda aka tauye masa hakki.
Umar danHadeja 08123122946 ya rubuto wasikarsa daga Malam-Madori, Jihar Jigawa.