Al’umma na da laifi kan yawaitar shaye-shaye – Ibrahim Katsina

Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina shi ne Shugaban Gidauniyar Samar da Zaman Lafiya da Tsaro a Zamantakewar Al’umma. A makon jiya ya kasance babban bako mai jawabi a taron Kungiyar Gizago ta Kasa a Katsina, inda ya gabatar da takarda kan illolin tu’ammali da miyagun kwayoyi. Aminya ta tattauna da shi dangane da wannan matsala ta […]

Al’umma na da laifi kan yawaitar shaye-shaye – Ibrahim Katsina

Ibrahim Katsina

Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina shi ne Shugaban Gidauniyar Samar da Zaman Lafiya da Tsaro a Zamantakewar Al’umma. A makon jiya ya kasance babban bako mai jawabi a taron Kungiyar Gizago ta Kasa a Katsina, inda ya gabatar da takarda kan illolin tu’ammali da miyagun kwayoyi. Aminya ta tattauna da shi dangane da wannan matsala ta shaye-shaye:

Wani al’amari da ya dade yana ci wa al’umma tuwo a kwarya da  yi mata barazana, shi ne shaye-shayen kwayoyi da kayan maye, me za ka ce game da haka?

A gaskiya wannan al’amari ne da dole hankalin kowa ya tashi a kai, kuma abu ne da ya wajaba kowa ya mai da hankalinsa a kai. Matsalar ma ita ce, hakan ya zama hantsi leka gidan kowa. Idan ba mu mai da hankali ba,  mun tashi tsaye ba, karshenta za a wayi gari matasanmu sun lalace, kuma ba laifinsu ba ne, laifinmu ne. Mun bari tu’ammali da kwaya ta koma makarantu da masana’antu da gidajenmu na matan aure, kowa sha yake. Ka ga wannan illa ce da idan aka kyale ta ci gaba,  al’umma za ta rushe.

Me kake ganin ya jawo tu’amali da kwaya a al’ummarmu, musamman matasa?

Rashin kula, domin  al’umma ba ta damu da abin da ke damun matasanta ba. Shi matashi sanya shi hanya ake yi, idan ba ka sanya shi hanya ba, zai sama wa kansa hanya. Akwai wani abin da Bature ke cewa “curiosity” wato kokarin mutum ya gano shin me ake ciki? Ka san a duk lokacin da mutum ke tasowa yana karami, akwai wannan dabi’ar. Shi matashi bai san ciwon kansa ba, hanyar da ka sa shi, ita zai bi. Idan ka kyale shi sai ya samar wa kansa hanya kuma mafi yawanci hanyoyin da matasa suke bi, ba su san inda za su ba, na farko ke nan da ke kawo shaye-shaye ga matasa. Na biyu shigowar kakar siyasa, domin ’yan siyasa sun ga cewa idan ba sun saka matasa ga shaye-shaye ba, ba za su yi musu banga ba saboda mai hankali ba za a yi banga da shi ba. To, wannan ya kara haddasa tu’ammali da miyagun kwayoyi. Yanzu ta kai ga ba ma ’yan bangar siyasa ba, hatta daliban jami’a sha suke yi. Ka ga wannan ya sanya al’umma ce ta janyo wa matasa wannan illa.

Wadansu na ganin yawaitar kemis-kemis da wuraren sayar da magunguna ya jawo haka, me za ka ce?

Ba haka ba ne gaskiya, domin ai a Kudancin Najeriya akwai wuraren sayar da magani, amma sun yi wa matasansu alkibla. Mu ma abin da ya kamata ke nan, mu zauna mu yi wa namu matasan alkibla. Maganar kyamis-kyamis, ai suna da ka’idojin gudanarwa, kuma muna da hukumomi, to mene ne aikin hukuma idan ba za ta iya tafiyar da su bisa ka’idar da aka gindaya ba? Don haka samuwar kyamis ba shi ne illar ba, illar kawai ita ce al’umma ta zama kara-zube. Ba ka damu da abin da ya damu dan uwanka ba, idan ba na tsegumi ba ne. A ce mu zauna ka ga dan makwabcinka ya yi kyau, a da mu lokacin da muke kanana, makwabcinka zai tattara ku a yi muku shayi (kaciya), a kai ku makaranta, yanzu ana wannan? To ba maganar yawan kyamis ba ce, rashin sanin ciwon kai ne na al’umma. Idan al’umma ta san ciwon kanta, shaye-shaye zai zama tarihi.

Wace shawara za ka ba gwamnati daga tarayya zuwa karamar hukuma kan yadda za a magance batun shaye-shaye?

Mun fara da Gwamnatin Jihar Katsina, muna kawance da ita wajen ganin an fadakar da al’umma illolin shaye-shaye. Kamar irin wannan taron na yau da Kungiyar Gizago ta gudanar da kungiyoyin sa-kai da sarakuna da malaman addini, a fadakar da su su gane illar matsalar, a yarda cewa akwai ta. Na biyu, a hadu kowa ya ba da gudunmawa, mu jawo matasan nan a jiki. Wato idan aka ce za a bar gwamnati ita kadai, ba za ta iya ba.

Al’umma ya kamata mu hadu  da gwamnati, mu fuskanci abin da ya kamata a yi na fadakar da al’umma su san illar wadannan abubuwa. Sannan a sanya kwamitoci tun daga unguwanni zuwa yanki zuwa karamar hukuma zuwa jiha, yadda jama’a ne za su hadu a tsarin al’umma. Amma idan aka bar gwamnati ba za ta iya ba, ai masu kyamis-kyamis din ’ya’yanmu ne, shagunan namu ne saboda haka a samar da tsarin kulawa domin mu yi wa kanmu Kiyamul Laili, kowa ya kasance ya zama dan sandan kansa yadda za a taimaka.

Gwamnati in ta tabbatar da cewa ta hada kan al’umma haka, kamar yadda suke yi a Kudu – me ka yi wa al’ummarka? Wato hadin kai a tsakanin al’ummar gari, mu rika haduwa kamar lokacin Sallah, dan kowace unguwa, dan kowane gari mu gano me ke damunmu? Ta haka za a samu nasara, gwamnati abin da za ta yi ke nan, sai wahala ta ragu a wajenta. Amma idan aka bar mata komai, ba ta da isassun jami’an da za su yi mata wannan aiki.

Sarakuna da malaman addini wace rawa za su taka?

Yauwa, ka ga kamar abin da Sarkin Katsina da na Daura ke yi wajen fadakar da al’umma, wannan yana da muhimmanci kuma ya kamata a karfafa musu. Na biyu, malaman addini a wurin wa’azi, abin da za su rika fadakar da mutane shi ne, mu san ciwon kanmu, mu hada kanmu kuma mu taimaki kanmu. Idan muka yi haka sai ka ga kowa ya farga, matasan nan mun ceto su saboda su ne rayuwarmu nan gaba. Matasan nan kada mu bari su lalace, don haka da malaman addini da sarakuna da masu mulki da kai da ni mu hada hannu mu hada kan al’umma mu fadakar da matasanmu. Idan aka yi haka za mu samu sauki.

Gidauniyarka ta Peace Builders, me kuka yi a baya, me kuke yi  yanzu, kuma me za ku yi nan gaba domin ganin an magance matsalar shaye-shaye?

Alhamdulillahi, yanzu muna kan fadakarwa ta hanyar tarurruka. Misali a nan Katsina, mun yi a shiyyar Katsina, mun yi a shiyyar Daura, za kuma mu yi a Funtuwa. Muna hada dukan al’umma da ’yan boko da malamai da ’yan siyasa da gwamnati, a san cewa ga abin da ya kamata, ga abin da ke damun al’umma. Mun fara wannan, sannan mun bi jami’o’i da makarantu muna fadakarwa kan illar shaye-shaye, domin samar da dauwamammen zaman lafiya. Kuma muna hada gwiwa da kungiyoyin sa-kai a sassan kasar nan wajen jawo hankalin jama’a kan illar wannan abu, domin a gyara, jama’a ta yi kyau.

A karshe wane kira kake da shi ga al’umma kan matsalar shaye-shaye?

Kirana ga al’umma shi ne, lallai ne mu farka, kowa ya duba ya ga wace gudunmawa ya ba da ko zai ba da don taimaka wa al’umma, ta hanyar wata dama da Allah Ya ba shi. Manzon Allah (SAW) ya ce “Kowanenmu mai kiwo ne.” Idan kowa ya yi abin da ya dace, to kasarmu za ta zauna lafiya.