Al’umma sun nemi gwamnatin Gombe ta gyara hanyar Gona–Tukulma

Al’ummar yankin sun koka kan yadda lalacewar hanyar ka iya tsayar da al’amuran yau da kullum.

Al’umma sun nemi gwamnatin Gombe ta gyara hanyar Gona–Tukulma

Al’ummar garin Tukulma da ke Ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe, sun roƙi gwamnatin jihar da ta gyara hanyar Gona zuwa Tukulma sakamakon lalacewar da ta yi.

Wani mazaunin yankin, Isah Hussaini Tukulma, wanda ya yi magana a madadin al’ummar garin, ya ce hanyar ta lalace matuƙa kuma tana jefa mutane cikin wahala.

Ya ce idan ba a gyara hanyar cikin gaggawa ba, akwai yiwuwar ta yanke gaba ɗaya, lamarin da zai ƙara tsananta matsalolin zirga-zirga ga mazauna yankin.

A cewarsa, Tukulma na daga cikin manyan garuruwan Ƙaramar Hukumar Akko, inda yawancin mutane ke dogaro da noma da kiwo wajen samun abin dogaro da kai.

Ya bayyana cewa lalacewar hanyar na kawo cikas ga safarar amfanin gona da dabbobi zuwa kasuwanni, abin da ke haddasa asarar kuɗi da ɓata lokaci ga manoma da ’yan kasuwa.

“Wannan hanya tana da muhimmanci sosai ga al’ummar yankin. Idan aka gyara ta, za a samu sauƙin kai amfanin gona da dabbobi zuwa kasuwanni, kuma harkokin kasuwanci za su bunƙasa,” in ji shi.

Isah, ya yaba da ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke aiwatarwa a sassa daban-daban, amma ya roƙi gwamnan da ya saurari koken al’ummar Tukulma tare da ɗaukar matakin gyara hanyar kafin matsalar ta ƙara muni.

Ya kuma ce dubban mutane ne ke amfani da hanyar a kullum, yana mai cewa gyaranta zai taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga da bunƙasa tattalin arziƙin yankin.