Al’umma ta koka da rashin bankuna a Potiskum

Garin Potiskum shi ne babbar cibiyar kasuwancin Jihar Yobe, gari ne da yake da dimbim jama’a, ‘yan Kasuwa da Ma’aikatan Gwamnati, wannan shi yasa mafi yawan bakunan kasar nan suka bude rassansu a garin na Potiskum. To amma a shekaru biyu da suka gabata, lokacin da harkokin tsaro suka tabarbare a Arewacin Najeriya ciki kuwa […]

Al’umma ta koka da rashin bankuna a Potiskum
Al’umma ta koka da rashin bankuna a Potiskum

Garin Potiskum shi ne babbar cibiyar kasuwancin Jihar Yobe, gari ne da yake da dimbim jama’a, ‘yan Kasuwa da Ma’aikatan Gwamnati, wannan shi yasa mafi yawan bakunan kasar nan suka bude rassansu a garin na Potiskum. To amma a shekaru biyu da suka gabata, lokacin da harkokin tsaro suka tabarbare a Arewacin Najeriya ciki kuwa har da Jihar Yobe, wanda har takai ga an kone mafi yawan bankunan da ke garin na Potiskum.
daya ne rak (First Bank), yake aiki a garin na Potiskum, duk da ma dai bankuna kamar su Diamond Bank da  Eco Bank da Finland Bank, su duk ba kona su ba, amma sun rufe sun daina hada-hadar kasuwanci. First Bank shi kadai ya rage a kaf fadin garin Potiskum, kuma yana fara aiki ne daga karfe tara na safe zuwa karfe 2 na azahar. Yadda jama’a suke tururuwa a wannan banki abin sai wanda ya gani, ana matukar shan wahala, musamman ma a layin cirar Kudi na na’urar  ATM.
karfe tara na safe ake bude Bankin, amma tun karfe bakwai na safen za ka ga dafifin  jama’a a wajen bankin, suna jira lokaci ya yi a bude. Lokacin na cika kuwa za a bude bankin, sai kuma jama’a su yi layi a fara shiga daya bayan daya, sai an fi awa guda da rabi ana shiga bankin layin bai kare ba. Sannan idan ka shiga ciki ba masaka tsinke, mutane ne cike makil kowa yana gudanar da abin da ya kawo shi.
  Jama’a sun fi shiga tashin hankali idan aka ce albashin ma’aikata ya shiga, mutum sai ya shafe kwana hudu yana wuni a banki, amma bai samu ya cire albashin nasa ba, saboda tsantsar cukowar jama’a. Wasu kuwa tafiya suke yi wasu garuruwa su curo kudinsu, ko kuma su saka, mafi yawan mutane suna tafiya garin Azare ne, wasu kuma Damaturu da Misau da Gombe ko Bauchi. Don kuwa mutum zai iya tafiya garin Bauchi ya curo kudi ya dawo, wanda yake layi a First Bank a Potiskum bai samu ya ciri kudin ba.
  Na ci karo da wani ma’aikacin gwamanti, ya gaji tilis a layin cirar kudi na ATM, mai suna Malam Baytah Mu’azu, inda ya ce “Gaskiya muna matukar shan wahala sosai idan muka zo cire albashinmu, yau kwana na uku cur ina zuwa wannan Banki domin in cire kudi, amma bana samun cirewa saboda cunkosan jama’a, kuma Bankin da nake aiki da shi Keystone Bank ne, ka ga dole ne in tsaya in bi wannan layi, in kuma ba zan tsaya ba, to ya zama dole in tafi wani gari in cire ke nan.”
  Shi ma Alhaji Shu’aibu Muhammad, wani dan kasuwane da yake gudanar da kasuwancinsa a babbar kasuwar Potiskum, na ci karo da shi ne a cikin Bankin, yana kokarin saka kudi a asusun abokan sana’arsa, domin a turo masa kaya, inda ya ce “Al’amarin Banki ya tabarbare a Potiskum, muna shan wahala sosai wurin tura kudi, saboda abokan huldarmu na kasuwanci da ke Kano ko Maiduguri, wasu suna amfani da First Bank, amma mafi yawansu ba da First Bank suke mu’amala ba, dole sai dai in biya wa daya daga cikin yarana kudin mota ya je gari mafi kusa da mu yasa musu kudi. Lokacin da muke da Bankuna da yawa a nan Potiskum, ba sai mun je sari da kanmu ba, da zarar mun yi waya ga abin da muke so, shi ke nan, sai a turo mana kaya, mu kuma mu tura musu kudi, amma yanzu matsalar Bankin nan ta tsayar da abubuwa da yawa, sai dai Allah Ya kawo mana karshensa”
“Banki daya rak a gari kamar wannan (Potiskum) ai kasan dole a sha wahala sosai wurin cire kudi, kuma ga shi wata rana ATM mashin din ba ya karbar kowane kati na ATM, sai na First Bank kadai. Wata rana kuma mu gama shan wahala a layi, sai mun yi dab da jikin mashin din sai ace mana kudi ya kare, gaskiya dai muna shan wahala da matsalar Bankin nan” inji Malama Sadiya, ma’aikaciyar Asibiti a garin Potiskum.

Ibraheem El-Tafseer, Potiskum 08032076472, [email protected]

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna