Al’ummar Agege sun samu sabuwar makabarta
A yanzu burin da al’ummar Agege a Legas suka daxe suna yi na mallakar sabuwar makabarta ya cika, domin kuwa Allah Ya share masu hawaye, inda cinikin sabuwar makabartar da kungiyar Fauzin Azim ta yi ya tabbata; bayan da a da aka yi ta yin tababarsa a lokacin da ake ganin kamar cinikin yana kasa […]
A yanzu burin da al’ummar Agege a Legas suka daxe suna yi na mallakar sabuwar makabarta ya cika, domin kuwa Allah Ya share masu hawaye, inda cinikin sabuwar makabartar da kungiyar Fauzin Azim ta yi ya tabbata; bayan da a da aka yi ta yin tababarsa a lokacin da ake ganin kamar cinikin yana kasa tana dabo.
Shugaban kungiyar matasan da suka yi tsayin daka don ganin an samu mallakar sabuwar makabarta a Agege, Malam Auwal Sani wanda wanda aka fi sani da Alfa Auwalu, ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu cinikin sabuwar makabarta ya tabbata kuma an yi nisa a aikinta, domin an kankare buraguzai da matacciyar kasar wurin, an kuma yi ciko inda aka zuba kasa tifa 400, kwatankwacin tan dubu takwas kuma ana kan kewaye wajen da katanga da kuma aikin kwalbati da magudanan ruwa. Ya ce da zarar an kammala aikin za su danka ta ga kungiyar Fauzun Azim da kuma masarautar Agege, domin a fara binne mutane a ciki. Ya kuma ce za a bar tsohuwar makabartar ta huta kafin a sake juyowa kanta.
Alfa ya ce an samu nasarar aikin ne bayan da sarkin samarin Agege, Alhaji Iro Garban Tafida ya ba su sahawarar zakulo waxanda za su ba da gudunmawa. “Sai muka yi zaman tattaunawa a gidansa da wasu jama’a kimanin mutum 20. Ba mu tashi daga wannan zama ba sai da muka haxa kuxi Naira miliyan 10 kuma da wannan kuxi ne muka fara aikin. Da mutane suka ga an fara aiki gadan-gadan sai su ma suka yi ta ba da gudunmawa, taimako yana ta fitowa ta ko’ina. Albishir xin da zan yi wa mutanen Agege shi ne, Allah Ya yaye mana masifar da muke ciki ta karancin wajan bine mutane kuma nan ba da daxewa ba za a fara amfani da sabuwar makabarta.” Inji Alfa Auwalu.