Al’ummar Agege sun tallafa wa fursunoni a Legas
Al’ummar Musulmin yankin Agege da ke Jihar Legas, sun kai ziyara gidan yarin kirikiri inda suka tallafa wa fursunonin da ke gidan da kayayyakin abinci da na masarufi don su ji dadin ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar sauran mutane. Da yake yi wa Aminiya karin bayani dangane da ziyarar a karshen makon da […]
Al’ummar Musulmin yankin Agege da ke Jihar Legas, sun kai ziyara gidan yarin kirikiri inda suka tallafa wa fursunonin da ke gidan da kayayyakin abinci da na masarufi don su ji dadin ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar sauran mutane.
Da yake yi wa Aminiya karin bayani dangane da ziyarar a karshen makon da ya gabata, daya daga cikin shugabannin tawagar, Alhaji Umar Lawan Atana ya bayyana cewa sun yanke shawarar tallafa wa fursunonin don rage musu radadin zaman gidan yarin.
“Taimaka wa wadanda suke zaune a gidan yari, musamman ma Musulmi ’yan uwanmu ya zama wajibi a gare mu, saboda haka sai muka yi yinkuri don ganin cewa mun nemi taimako daga wurin al’ummar Musulmi kuma mun gode wa jama’a saboda amsa kiran da suka yi, inda suka taimaka da kudi da kayan abinci da kayayyakin sa wa da magunguna da makamantansu.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Mutane sun taimaka, masallatai ma na khamsu salawatu da na Juma’a duk sun taimaka kwarai da gaske. A lokacin da lamarin ya taso na tuntubi mutanen gidan yarin inji irin abubuwa da fursunonin suke so sai suka gaya mani cewa suna bukatar abinci da kayan sa wa da magunguna. A yanzu zancen da nake yi da kai mun kashe kudi masu yawa wajen sayan kayayyakin da suka kamata.”
Ya bayyana cewa kwamitin wanda ya hada gwiwa da kungiyar Izala reshen Jihar Legas, ya isar da sakon da mutane suka bayar ga fursunonin.
Sannan kuma ya bayyana cewa kwamitin zai ci gaba da ziyartar gidan yarin don tallafa wa fursunonin.
daya daga cikin shugabannin kwamitin, Malam Alasan ya bayyana cewa kwamitin ya cin ma nasarori masu yawa. Ya yaba wa mutanen Agege dangane da gudunmawar da suka bayar don tallafa wa fursunoni da ke gidajen yarin Legas.